Diyar Gwamna Ganduje Ta Kara Maka Tsohon Mijinta a Gaban Kotu
- Ɗiyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta sake kai ƙarar tsohon mijinta a gaban wata kotun majistare a birnin Kano
- Asiya Abdullahi Umar Ganduje ta na ƙarar tsohon mijinta, Inuwa Bala a gaban kotun ne kan zargin laifuka shida
- Majistaren kotun ya ɗage sauraron ƙarar bayan Bala ya musanta aikata laifukan da tsohuwar matar ta sa ta kai shi gaban kotu saboda su
Jihar Kano - Asiya Abdullahi Umar Ganduje, ɗiyar gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta ƙara shigar da sabuwar ƙara akan tsohon mijinta, Inuwa Bala, a gaban wata kotun majistare a birnin Kano.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an gurfanar da Bala ne a gaban alƙalin kotun majistare 69, Ishaq Abdu Aboki, mai zamanta a kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, kan zargin laifuka shida.
Ko da rajistaran kotun, Nura Ahmad Yakasai, a dalilin rashin zuwan lauyan mai ƙara, ya karanto laifukan da a ke tuhumarsa da su, Bala ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su.
Lauyoyin da ke kare wanda ake ƙarar sun nemi kotu da ta bayar da belin wanda ake ƙarar inda suka kafa hujja da sashi na 3C na kundin tsarin mulki na shekarar 1999 da kuma sashi na 168, 172, 175 na ACJL.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majistaren ya bayar da belin wanda ake ƙara kan kuɗi N50,000, tare da sharaɗin kawo mutum biyu waɗanda za su tsaya masa, wadanda dole sai sun kawo hotunansu da wani abu da za a iya amfani da shi wajen gane su.
Sai dai, majistaren ya kuma ɗage ƙarar har zuwa ranar 25 ga watan Mayun 2023, domin cigaba da sauraron ƙarar, rahoton The Nigeria Lawyer ya tabbatar.
"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru
Matar Aure Ta Yi Yunkurin Halaka Diyar Makwabcinta a Kano
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta yi yunƙurin halaka ɗiyar makwabcinta a jihar Kano, saboda yana ba mijinta shawara ya ƙaro aure.
Matar auren dai mai suna Fatima Malam, ta caccakawa cikin ƙaramar yarinyar wuƙa da niyyar raba ta da duniyar nan. Fatima ta yaudari yarinyar ne da nufin za ta rakata wata unguwa a cikin birnin, inda daga nan ta aikata wannan aika-aikar.
Asali: Legit.ng