Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ma'aikatan NRC, Sun Aiko Da Sako Mai Daga Hankali

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ma'aikatan NRC, Sun Aiko Da Sako Mai Daga Hankali

  • Yan bindiga sun sace ma'aikatan hukumar sufurin jiragen kasa (NRC) su biyu a Agbor, jihar Delta
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kira waya, sun nemi a tattara musu miliyan N40m a matsayin kudin fansa
  • Kakakin tashar jirgin ƙasa da ke Agbor, ya ce a halin yanzun 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro na kokarin shawo kan lamarin

Delta - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla ma'aikatan hukumar sufurin jiragen kasa ta ƙasa (NRC) guda biyu a tashar jirgin kasa ta Agbor, jihar Delta.

Punch ta rahoto cewa waɗanda suka shiga hannun maharan sun haɗa da Peter Osazuwa, STCI, da kuma Giwa Mohammed, ɗan asalin jihar Kwara.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ma'aikatan NRC, Sun Aiko Da Sako Mai Daga Hankali Hoto: Punchng
Asali: UGC

Wata majiya daga cikin ma'aikatan NRC, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce waɗanda yan bindiga suka sace suna aiki ne da jirgin kasan Warri-Itakpe a Agbor.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Ayarin Gwamnan APC Ya Gamu da Mummunan Hatsari, Mutum Uku Sun Mutu

Ya ce lamarin ya faru wurin da bai wuce tafiyar 'yan mintuna ƙalilan daga garin Owa-Alero, garin kakannin gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shin maharan sun nemi kuɗin fansa?

Mutumin ya ce:

"Sun shiga hannun masu garkuwa ranar Alhamis da yamma a Owa-Oyibu a hanyar dawowa daga garin, inda suka je sayen wasu kayan abinci. An farmake su a mahaɗar Titin zuwa kasuwar Abavo."
"Tayoyin Motar Jeep ɗin da suke ciki sun yi kaca-kaca, an farfasa gilasan Motar kafin daga bisani aka yi awon gaba da su."
"Ba'a daɗe ba masu garkuwan suka kira mutanen dake da kusanci da tashar jirgin ƙasan Agbor, kuma sun nemi a haɗa musu miliyan N40m a matsayin fansa."

Wata majiya ta ƙara cewa harin ya jefa baki ɗaya mazauna Agbor cikin tashin hankali da firgici.

Kara karanta wannan

"Ta Yaya Ta Aikata Hakan?": Matashiyar Budurwa Ta Yi Amfani Da Takardun Bogi Wajen Siyo Dalleliyar Motar N8m

Wane mataki hukumomin tsaro suka dauka?

Yayin da aka tuntubi kakakin NRC na tashar jirgin Agbor, Olanrewaju Oke, ya ce yanzu haka 'yan sanda da hukumomin tsaro suna kokarin shawo kan lamarin.

"Tuni aka faɗa wa shugabanni abinda ya faru amma ba zan iya cewa komai ba saboda Manaja baya nan," inji shi.

Yan bindiga sun ƙara kai hari Abuja

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Mummunan Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 15 a rukunin gidaje 1,000 da ke a ƙauyen Pegi, a daren ranar Lahadi, cikin ƙaramar hukumar Kuje ta birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262