Rantsar Da Tinubu: Za Mu Bada Cikakken Tsaro, Babagana Monguno
- Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya ba da tabbacin samar da tsaro a yayin bikin rantsar da Bola Tinubu
- Monguno ya ba da tabbacin ne yayin wani babban taro a Abuja don shirye-shiryen bikin a ranar Alhamis
- Ya kirayi ‘yan Najeriya da su gujewa duk wasu abubuwan da za su kawo tsaiko a wurin bikin rantsarwar
Abuja - Mai bada shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin samar da tsaro yayin bikin kaddamar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.
Monguno ya ba da wannan tabbacin ne yayin wani babbban taro a Abuja wanda aka gudanar don shirye-shiryen bikin a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu.
Babagana wanda ya ke jagoranatar kwamitin tsaro a shirye-shiryen mika mulki wa sabuwar gwamnati ya ce sun dauki tsauraran matakai don ganin an samu tsaro a yayin bikin, jaridar Punch ta tattaro.
Monguno ya ce tsaro zai yalwata a Eagle Square
Ya ce za a samar da kyakkyawan tsaro a farfajiyar Eagle Square da kuma wuraren da ke kusa wadda anan ne za a gudanar da bikin a ranar 29 ga watan Mayu, cewar jaridar Ripples.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Tabbas wannan abin yana da muhimmanci musamman duba da yadda wadannan kwamitoci suke.
“Shi yasa muka dauko mambobin kwamitocin daga ko wane bangare na tsaron kasar nan."
Ya kara da cewa:
“Babban hafsan tsaro da babban sifetan ‘yan sanda da kuma shugaban hukumar tsaro ta farin kaya da gwaman jihar Kebbi wanda shi yake wakiltar gwamnatin da za a rantsar.
“Babban abin da za muyi shine samar da tsaro a wurin bikin da kuma otal din da baki da manyan mutane za su zauna har zuwa lokacin kammala bikin."
Ya yi magana akan zirga-zirgan mutane
A bangaren hana zirga-zirga a kusa da wurin taron, Monguno ya tabbatar da cewa ba za a bar zirga-zirgar ababen hawa ba saboda dalilai na tsaro, Pulse ta tattaro.
Yayin da ya tabbatar cewa an samar da wasu wurare da masu zirga-zirgar ababen hawa ko da sawu za su bi don samun sauki.
Ya ba da tabbacin gudanar da taron lafiya, yayin da ya bukaci ‘yan Najeriya da su gujewa duk abubuwan da za su kawo katsalandan a wurin taron da ma kasa baki daya.
Kotu Ta Ki Ba Da Belin Mai Zanga-Zangar Adawa Da Rantsar da Tinubu a Abuja
A wani labarin, wata kotu dake Abuja ta ki bayar da belin Obiajuli Uja bisa zargin tada tarzoma a filin jirgi.
Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ba za a rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu ba.
Asali: Legit.ng