Fitaccen Dan Jarida Kuma Tsohon Sanatan Jam'iyyar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Fitaccen Dan Jarida Kuma Tsohon Sanatan Jam'iyyar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Jihar Ebonyi ta yi babban rashin fitaccen ɗan jarida kuma tsohon sanata wanda ya koma ga mahaliccinsa
  • Sanata Anyim Chukwu Ude, ya yi bankwana da duniya ranar Litinin, 15 ga watan Mayun 2023 yana da shekara 82
  • Tsohon sanatan kafin mutuwarsa ya yi aiki da gidajen watsai labarai da dama a ƙasar nan inda ya samu ƙwarewa sosai

Jihar Ebonyi - Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon sanata wanda ya wakilci Ebonyi ta Kudu, Anyim Chukwu Ude, ya yi bankwana da duniya.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, Nnanna Ude, ɗan marigayin ya bayyana cewa mahaifinsa ya mutu ne a ranar Litinin, amma bai yi ƙarin haske ba kan dalilin mutuwarsa.

Tsohon sanata Anyim Chukwu Ude ya mutu
Anyim Chukwu Ude ya mutu yana da shekara 82 a duniya Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Ude wanda aka haifa a ranar 1 ga watan Yunin 1941, ya mutu yana da shekara 82 a duniya.

Kara karanta wannan

"Ta Yaya Ta Aikata Hakan?": Matashiyar Budurwa Ta Yi Amfani Da Takardun Bogi Wajen Siyo Dalleliyar Motar N8m

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Cike da baƙin ciki da nuna godiya ga ubangiji, iyalanmu na sanar da mutuwar mahaifinmu, sanata Anyim Chukwu Ude, MON,"
"Wanda aka haifa a ranar 1 ga watan Yunin 1941, ya bar duniyar nan domin haɗuwa da ahalinsa a ranar Litinin, 15 ga watan Mayun 2023."

Ya yi aiki a wurare daban-daban

Fitaccen ɗan jaridan ya zama sanata ne daga shekarar 2007 zuwa 2011.

Ƙafin ya tsuduma cikin harkar siyasa, Ude ya yi aiki gidajen jaridu da talbijin da dama, inda ya fara aiki da Nigerian Outlook a shekarar 1965, rahoton The Sun ya tabbatar.

Ya yi aiki a wurare da dama da suka haɗa da, East Central State Broadcasting Service (ECBS), Nigerian Television Authority (NTA), Imo Broadcasting Service (IBS) da Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN).

Kara karanta wannan

Rai Ya Yi Halinsa Yayin Da Fada Ta Barke a Tsakanin Jami'an EFCC a Sokoto

An yi wa mamacin kwamishinan kasuwanci na jihar Ebonyi, a shekarar 1999.

Najeriya Ta Yi Rashin Gogaggen Dan Jarida

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa an yi rashin gogaggen ɗan jarida, Peter Enahoro, aka fi sani da sunan Peter Pan.

Peter Enaharo yana ɗaya daga cikim fitattun ƴan jaridar da ake ji da su a ƙasar nan da ma nahiyar Afrika gaba ɗaya. Enahoro haifaffen jihar Delta, ya yi bankwana da duniya yana da shekara 88.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng