Shugaba Buhari: Cikas 1 da Ya Hana Ni Maganin Barayin Gwamnati a Mulkina

Shugaba Buhari: Cikas 1 da Ya Hana Ni Maganin Barayin Gwamnati a Mulkina

  • Irin satar da ake tafkawa a Gwamnatin Najeriya ta ba har Shugaba Muhammadu Buhari mamaki
  • Malam Garba Shehu ya ce dokar kasa ta yi wa mai gidansa dabaibayi wajen yakar barayin kasar nan
  • Mai magana da bakin shugaban kasar ya ce har yau babu wanda ya yi wa Buhari shaidar rashin gaskiya

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta nuna Muhammadu Buhari ya girgiza da ya ga irin kasurgumar sata da rashin gaskiya da suka dabaibaye Najeriya.

Mai girma Muhammadu Buhari ya shaida haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu a lokacin da aka yi hira da shi a tashar Channels.

Malam Garba Shehu ya nuna lamarin rashin gaskiya a kasar ya wuce yadda mutane su ke tunani.

Fadar Shugaban Kasa
Muhammadu Buhari ya dawo gida Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin zai yaki barayin gwamnati, har yanzu da yake shirin barin ofis, ba a shawo kan matsalar ba.

Kara karanta wannan

Wayau Za A Yi Wa Tsoho: Zan Je Kotu In Hana Bashin Karshe Da Buhari Yake So, Sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce har gobe mai gidansa mutumin gaskiya ne kuma bai da wani asusu da ya boye kudi a ko ina a kasar waje.

Abin da Garba Shehu ya fada

"Idan ka tambayi shugaban kasa (Muhammadu Buhari) wannan tambaya (meyasa har yanzu ake fama da rashin gaskiya a kasar nan)
Shi ma zai ce ya na mamakin yadda wadanda ya kamata a ce su na gidan yari, su na tuka Rolls Royce, su na yawo a cikin jiragen sama.

- Garba Shehu

A dokar kasa, Garba Shehu ya ce babu abin da bangaren zartarwa zai iya illa ya yi bincike, sannan a gurfanar da duk wanda ake zargi da rashin gaskiya.

Hadimin shugaban kasar ya ce daga an kai magana zuwa kotu, su kuma sun gama na su kokarin.

An rahoto Mai magana da bakin shugaba mai barin-gadon ya na cewa kotu ce za ta iya yankewa mutum hukunci idan ya na da laifi ko kuwa akasin haka.

Kara karanta wannan

Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Shake da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu

A gwamnatin Buhari ana binciken har manyan gwamnati, Shehu ya ce hakan ya nuna gwamnati mai-ci ta yi bakin kokarinta wajen yakar rashin gaskiya.

Antony Blinken ya kira Tinubu

Dazu nan aka samu labari daga Tunde Rahman cewa Asíwájú Bola Tinubu ya yi magana da Sakataren gwamnatin Amurka, Antony Blinken ta salula.

Zababben shugaban kasar ya fadawa Blinken cewa abin da zai fara da su a mulki su ne gyara hukumomin gwamnati da kokarin taimakon marasa karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng