Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

  • A wani karon na dabam, Mataimakin shugaban Najeriya ya jagoranci zaman FEC a fadar Aso Rock
  • A taron ne Farfesa Yemi Osinbajo ya amincewa ‘yan kasuwa sua kafa wasu karin jami’o’i a kasar nan
  • Ministan ilmi ya sanar da haka ba tare da yin cikakken bayanin inda za a samar da makarantun ba

Abuja - Mataimakin shugaban Najeriya, Mai girma Yemi Osinbajo ya amince ‘yan kasuwa su kafa wasu sababbin jami’o’i 36 a kasar nan.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bada damar kafa jami’o’in ne a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar FEC kamar yadda The Nation ta rahoto.

A maimakon a zauna a ranar Laraba yadda aka saba a kowane mako, gwamnatin tarayya ta kira taron FEC na musamman a ranar Litinin.

Shugaban Kasa
Ministoci a taron FEC Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Buhari bai dawo ba har yanzu

Wannan yana cikin taron da Ministoci da manyan mukarraban gwamnati suka yi alhali Muhammadu Buhari bai iya samun halarta ba.

Kara karanta wannan

Pantami da Wasu Ministocin Buhari 9 Da Za Su Iya Tsira da Kujerunsu a Mulkin Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu ya sanar da wannan cigaba da aka samu bayan zaman da Ministocin tarayya suka yi a birnin Abuja.

Malam Adamu yake cewa da wannan mataki da aka dauka, akwai jami’o’i 72 da ‘yan kasuwa suka mallaka, gwamnati ta na ganin cigaba ne.

An samu cigaba?

Ministan ya nuna an amince a kafa manyan makarantun ne bayan la’akari da yadda za a iya amfani da harkar ilmi a bunkasa tattalin arziki.

Majalisar zartarwa ta duba takardu 40 daga ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomi dabam-dabam, daga nan aka bada lasisin kawo sababbin jami’o’i.

Karatu ta yanar gizo

Ministan ya ce a cikin jami’o’in da aka kafa har da wanda za ta rika aiki ta yanar gizo, a karon farko kenan da aka kafa irinta a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

An rahoto Adamu yana cewa jami’ar da za a samar a jihar Bauchi za ta taimakawa musamman matan Arewa da ke kyashin gogayya da mutane.

A bayaninsa, Ministan ilmin bai fadi sunan jami’o’in da za a kafa ba, illa iyaka ya nuna akwai bukatar karin jami’o’i saboda masu sha’awar karatu.

Bukatun kungiyar CAN

Idan ya gaji Muhammadu Buhari, an ji labari kungiyar CAN ta na so Bola Tinubu ya girmama dokar daidaito wajen rabon mukamai da albarkatu.

Shugaban CAN ta Kiristocin kasar nan, Daniel Okoh ya ce ya zama wajibi a ba ‘yan kasa damar yin bauta da ibada ba tare da an tursasa masu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng