Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

  • Nan da makonni biyu ake sa ran rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya
  • Akwai wasu kalubalen da Gwamnatin Bola Tinubu za ta gada daga wajen Muhammadu Buhari
  • Sha’anin rashin tsaro da matsalar tattalin arziki yana cikin abubuwan da sai gwamnati tayi da gaske

Abuja - Ganin ana shirin nada sabon shugaban kasa, Legit.ng ta tattaro abubuwan da ake ganin za su iya ci wa gwamnati mai jiran mulki tuwo a kwarya.

Ga jerin nan kamar haka:

1. Rashin tsaro

An yi nasarar magance ta’adin Boko Haram, amma yanzu ana fama da rigimar makiyaya da manoma, ‘yan bindiga, da masu garkuwa da mutane.

Bola Tinubu zai ci karo da matsalar rashin tsaro musamman a yankin Kudu maso gabashin Najeriya da kuma wasu jihohin da ke Arewacin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

Bola Tinubu
Bola Tinubu tare da Hon. Tajudeen Abbas Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Tattalin arziki

Baya ga bashi da Tinubu zai nemi hanyar da za a biya, gwamnatinsa za ta fuskanci hauhawar farashin kaya, yunwa da talauci da masifar rashin aikin yi.

Jama’a na sa rai a gwamnati mai zuwa kayan abinci su yi araha, sannan Naira ta yi daraja bayan an shafe shekaru kusan takwas an gaza shawo kan Dala.

3. Yaki da rashin gaskiya

Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai yaki marasa gaskiya bayan ya karbi ragamar shugaban Najeriya daga hannun Shugaba Goodluck Jonathan.

Har yanzu gwamnati ba ta gama nasara ba, za a saurari yadda shugaba mai jiran gado za tayi wannan aiki tare da tunawa da wadanda suka taimaki APC.

4. Tallafin man fetur

A lokacin Olusegun Obasanjo da musamman Goodluck Jonathan, an yi kokarin janye tallafin fetur amma abin ya faskara, har gobe Najeriya ta na kashe Tiriliyoyi.

Kara karanta wannan

Yawaita Zuwa Turai: Tinubu zama zai yi ya mulki Najeiya, inji hadiminsa

Da zarar ya gaji Buhari, Tinubu ya yi alkawarin janye wannan tsari. Sai dai hakan zai yi sadadiyyyar tsadar rayuwan da za ta iya haddasawa gwamnati bakin jini.

5. Wutar lantarki

Gwamnati mai-ci ta kashe kudi maso yawo domin samar da wutar lantarki, amma duk da haka mutane su na zama cikin duhu musamman a kwanakin nan.

Za a so a ga yadda gwamnatin gobe za ta kawo gyara a wannan harka bayan saida kamfanonin rabon wutan yayin da irinsu aikin wutan Mambila suka gagara.

Shawarwarin Olusegun Mimiko

An samu labari Segun Mimiko ya fadawa Bola Tinubu ka da ya yi koyi da Muhammadu Buhari a wasu bangarori, daga ciki akwai rabon mukamai.

Mimiko ya bada shawarar akwai bukatar duba canjin kudi, tattalin arziki da tallafin fetur, yana ganin ba za ta yiwu a cigaba da kashe kudi da sunan tallafi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng