'Yan Ta'adda Sun Sake Halaka Mutane Bakwai A Jihar Kaduna
- Wasu wanda ake zargin makiyaya ne sun kai hari kauyen Warkan a yankin Atyap a karamar hukumar Zango Kataf
- Maharan sun kashe akalla mutane 7 da jilkkata wasu wanda ba a san iyakarsu ba a wannan yankin na Atyap
- Majiyarmu ta tabbatar da cewa maharan sun addabi wannan yanki kusan kullum sai sun kai musu hari
Jihar Kaduna – Ana zargin wasu makiyaya da kashe akalla mutane bakwai a kauyen Warkan na yankin Atyap a karamar hukumar Zangon Kataf da ke kudancin jihar Kaduna.
Jaridar Punch ta tattaro cewa ‘yan bindigan sun kuma kona gidaje da dama da salwantar da dukiyoyi masu yawa, yayin da wadanda suka samu raunuka ba za su misaltu ba.
Majiyarmu ta ce maharan sun durfafi kauyen lokacin ka kai harin suka ci karen su ba babbaka, yayin da mahukunta ke kokarin gano yawan mutanen da suka samu raunuka.
Rahoton ya ce abin bakin ciki shine yadda mahukunta ba sa daukan matakai masu tsauri da zasu dakile irin wadannan hare-haren da suke faruwa na tsawon lokaci musamman a yankin Atyap.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Mun gagara fahimtar yadda ake kai hare-hare akai-akai musamman a wannan yanki namu na Atyap, abin takaici shine yadda gwamnati a matakin jiha da ta tarayya suka gagara daukan tsauraran matakai don dakile wadannan hare-hare.” In ji majiyar.
Ba a samu bayani daga hukumomi ba
Kokarin da aka yi don samun martani dangane da harin daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Jalige ya ci tura.
Yayin da kwamishinan Tsaron Cikin Gida Samuel Aruwan shi ma ba a same shi ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.
Jihar Kaduna dai na fama da hare-haren 'yan bindiga da a kullum ke addabar yankunan jihar daban-daban musamman a kudancin jihar.
Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'ya da Jikokin Sarkin Kagarko a Kaduna
A wani labarin, Yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun durfafi fadar sarkin Kagarko, Alhaji Abubakar Sa'ad a kudancin jihar Kaduna, sun sace mutane da dama.
Maharan sun kutsa kai ne cikin fadar inda suka sace jikoki da kuma 'ya'yan sarkin guda tara kafin su fita a fadar su kuma sace wasu mutum uku daban a yankin.
Asali: Legit.ng