Yadda Ganduje Ya Tattara Kayan Gwamnati, Yana Saidawa Iyalinsa – Kwamitin Abba

Yadda Ganduje Ya Tattara Kayan Gwamnati, Yana Saidawa Iyalinsa – Kwamitin Abba

  • Kwamitin karbar mulkin Kano ya zargi Gwamna da yi wa mutane da iyalinsa gwanjon kayan gwamnati
  • Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya yi ikirarin Abdullahi Umar Ganduje ya saida ma’aikata ga wani yaronsa
  • Shugaban wannan kwamiti ya ce da zarar Abba Kabir Yusuf ya shiga ofis, zai karbo duk kadarorin al’umma

Kano - Kwamitin da Abba Kabir Yusuf ya kafa domin karbar mulkin jihar Kano ya zargi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da saida kayan gwamnati.

Legit.ng Hausa ta fahimci shugaban kwamitin, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya jefi Gwamnati mai barin gado da wannan zargi ne a yammacin ranar Laraba.

Abdullahi Baffa Bichi ya jagoranci jama’a zuwa ofishin wata ma’aikata da su ke zargin Abdullahi Umar Ganduje ya saida ta ga yaronsa, Abba Ganduje.

Ganduje
Dr. Abdullahi Baffa Bichi a gaban ma'aikata Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Jagoran na jam’iyyar NNPP ya ce har zuwa jiya, ma’aikatan gwamnari su ke amfani da ofishin, sai kwatsam aka ji cewa an yi gwanjonsa ga ‘dan Gwamna.

Kara karanta wannan

Ba a Haka: Inda Tinubu Ya Yi Kuskure Wajen Shugabancin Majalisar Dattawa – Sanata

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Bichi ya kamanta aikin gwamnatin APC da fasa-kauri, ya ce ana tattara kayan da ke ma’aikatar. Wasu hotuna da ke yawo a Facebook sun karfafa zargin.

Ma'aikata guda a N10m?

Daily Trust ta rahoto Bichi ya na fadawa Duniya cewa NNPP ta samu labari an saida daukacin ma’aikatar ne a kan farashin da bai kai Naira miliyan 10 ba.

Zuwa 29 ga watan Mayun 2023, shugaban kwamitin karbar mulkin ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta fara dawo da duk kadarorin da aka yi gaba da su.

Daga dukiyar gwamnati da aka sace zuwa wadanda aka karkatar ko aka lalata, NNPP ta sha alwashin za su bar hannun ‘yan daidaikun da suka amfana.

Kwamitin ya kuma gargadi ‘yan kwangila da su guji taimakawa a abin da ya kira aika-aika. Duk abin da yake faruwa, gwamnatin Kano ba tayi magana ba.

Kara karanta wannan

Kwana 18 Gabanin Rantsar da Tinubu, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Abin da ya faru a jiya

Kabiru Dakata ya yi magana a kan lamarin a shafinsa na Facebook, ya ce:

“Dazu mu na sakatariyar kwamitin karbar mulki, sai aka kiramu cewar ga shi chan an ce ma'aikatan Kano State Public Procurement Bureau su tashi an sayar da gurin.
Ina aka taba yin haka? Nan da nan jagororin babban kwamitin su ka dira gurin. Da nan gurin, da ireirensa kowa ya siya ya sayi WOFI.

- Kabir Dakata

An nemi tuntubar Kwamishinan labarai domin jin gaskiyar lamarin, amma jaridar ba ta same shi ba.

Shari'ar Abba v APC a Kano

A ranar Laraba, Legit.ng Hausa ta tattauna da Lauyan da ya ke kare NNPP, ya shaida mana za a kori karar jam’iyyar APC a kan zaben Gwamnan jihar Kano.

Barista Bashir Tudun Wazirci ya ce nasara ta jam’iyyar NNPP da mutanen Kano ce, ya ce batun an gano kuri’u marasa hatimi, zancen teburin mai shayi ne.

Kara karanta wannan

Ku Rungumi Kaddara, Basarake Ya Fadawa Masoyan Obi, Atiku, Su Bi Bayan Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng