Tsohon Shugaba Jonathan Ya Jinjinawa Buhari Saboda Abin da ya yi wa 'Yan Bayelsa
- Dr. Goodluck Jonathan ya yi jawabi da ake kaddamar da horon da NASENI za ta bada a Bayelsa
- Gwamnatin tarayya ta zabi matasa 100 da za a koyawa kanikancin wutar lantarki a garin Otuoke
- Jonathan ya ji dadin yadda hukumar NASENI ta ke kokarin rage masu zaman banza a mahaifarsa
Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yabi Muhammadu Buhari a dalilin kokarinsa na ganin mutane sun kafu da kafafunsu.
The Nation ta ce Dr. Goodluck Jonathan ya godewa Shugaba Muhammadu Buhari da ya bada umarni ga hukumar NASENI ta horas da matasan Bayelsa.
Jonathan wanda ya yi mulkin Najeriya daga 2010 zuwa 2015 ya fito ne daga jihar Bayelsa, inda za a ba matasa 100 hora a kan kimiyya da fasaha.
A ra’ayin Jonathan, rashin sanin kimiyya da fasaha ya taimaka wajen karancin cigaban Najeriya, don haka ya bada shawara a maida hankali a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban ya samu damar yin jawabi wajen kaddamar da shirin NASENI na koyawa matasa sana’a da aka yi a mahaifarsa ta Otuoke a Bayelsa.
The Guardian ta ce hukumar za ta koyawa mutanen da aka zaba dabarun aiki da wutar lantarki.
Kimiyya da fasaha ne mafita
Da yake gabatar da jawabinsa, tsohon Gwamnan na Bayelsa ya ce ‘kimiyya da fasaha' su ne sirrin duk wani cigaban tattalin arzikin gaggawa a kasashe.
Jonathan ya ce kasashen da suka cigaba, su na bada karfi a wadannan bangarori, don haka ya yi kira ga wadanda za a horas da su yi amfani da damarsu.
A yayin da ya yabi gwamnati mai-ci, Jonathan ya ja-kunnen matasan da cewa ka da su saida kayan aikin da aka ba su, wanda darajarsu sun kai miliyoyi.
Idan tsarin ya yi nasara, mutanen Otuoke za su kware a bangaren kanikancin lantarki, za au samu hanyar neman na kai, hakan zai rage zaman banza.
Sai an ba NASENI karfi
Mataimakin Darektan yada labarai na NASENI, Olusegun Ayeoyenikan ya fitar da jawabi cewa matakin da gwamnati ta dauka zai taimakawa matasa.
Olusegun Ayeoyenikan ya ce idan ba a kula da hukumomin bincike da fasaha irinsu NASENI, zai yi wahala a iya samun cigaba ta fuskar tattalin arziki.
Heritage Times ta karrama GEJ
A kwanakin baya, an samu labarin yadda Heritage Times ta shirya wani biki, ta ba shugabannin Afrika lambar yabo, daga ciki har da Goodluck Jonathan.
Jonathan ya samu kyautan zama Gwarzon Damukaradiyya da zaman lafiya. Kungiyar ta karrama John Magufuli, Jewel Howard-Taylor da Seretse Khama.
Asali: Legit.ng