Yan Bindiga Sun Kai Hari 'Hostel' Ɗin Dalibai Mata a Jami'ar Filato

Yan Bindiga Sun Kai Hari 'Hostel' Ɗin Dalibai Mata a Jami'ar Filato

  • Jami'ar jihar Filato (PLASU) ta tabbatar da rahoton yunkurin garkuwa da ɗalibanta amma maharan ba su samu nasara ba
  • Mai magana da yawun jami'ar, John Agams, ya ce dakarun tsaron makarantar ne suka kori 'yan bindigan ba tare da sun ɗauki ko mutum ɗaya
  • Ya ce mataimakin shugaban jami'ar (VC) ya shiga makarantar domin zubawa zukatan ɗalibai ruwan sanyi karsu ɗauki wani mataki

Plateau - Hukumar jami'ar jihar Filato (PLASU) da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ta tabbatar da cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari ɗakunan kwanan ɗalibai mata.

Ta ce 'yan bindigan sun kai harin a tsakanin daren ranar Talata, 9 ga watan Mayu zuwa wayewar garin Laraba da nufin garkuwa da ɗalibai mata, kamar yadda PM News ta rahoto.

Jami'ar PLASU
Yan Bindiga Sun Kai Hari 'Hostel' Ɗin Dalibai Mata a Jami'ar Filato Hoto: pmnewnigeria
Asali: UGC

Hukumar jami'ar ta bayyana cewa jami'an tsaron makarantar sun samu nasarar daƙile yunkurin 'yan bindigan jejin na shiga 'Hostel' ɗin mata tun kafin su ɗauki kowa.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Cafke Wasu Jami'an Tsaro Masu Aikata Fashi Da Makami

Yadda lamarin ya faru

Rahoton Daily Trust ya ce Jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar jihar Filato, Mista John Agams, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Agams ya ce 'yan ta'addan sun kai farmaki makarantar ne da nufin sace ɗalibai amma suka kwashi kashinsu a hannin jami'an tsaro, waɗanda suka daƙile harin.

"Eh dagaske ne, 'yan bindiga sun yi yunkurin ɗibar ɗalibanmu amma basu sami nasara ba, jami'an tsaron cikin jami'an ne suka kore su. Garin haka ɗaliba ɗaya ta ji rauni amma ba wanda maharan suka ɗauka."
"Mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Benard Matur, ya shiga cikin makaranta yanzu haka yana tausar zuciyoyin ɗalibai su zauna lafiya."

- John Agams.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ce har kawo yanzu hukumar yan sanda reshen jihar Filato ba ta ce komai ba game da wannan sabon harin.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan 'Yan Majalisa 5 Na APC Da Suka Lashi Takobin Yaƙar Ɗan Takarar Tinubu a Majalisa Ta 10

An kashe hatsabibin ɗan bindiga a Kaduna

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Muhammad Jalige, ya ve dakarun sun tari yan ta'adda, waɗanda suka snaya kakin soji a Kidandan, karamar hukumar Giwa.

Yayin musayar wuta, yan sanda suka sheke ɗan bindigan kuma suka kwato Babur guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262