Yan Ta'adda Sun Aika Ɗaya Cikin Mutanen Da Suka Sace Ya Siyo Musu Fetur A Neja

Yan Ta'adda Sun Aika Ɗaya Cikin Mutanen Da Suka Sace Ya Siyo Musu Fetur A Neja

  • Sojojin sun yi nasarar halaka aƙalla 'yan ta'adda 30 a wani farmaki da suka kai musu a dajin Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro jihar Neja
  • 'Yan ta'addan da suka zo akan babura sun farmaki ƙauyen na Allawa inda suka yi awon gaba da mutane huɗu da ke aiki a gonakinsu
  • Sojojin su samu bayanai ne daga gurin ɗaya daga cikin mutanen da 'yan ta'addan suka aiko ya siya musu mai da kuma kayan shaye-shaye

Neja - Sojoji sun yi luguden wuta tsakaninsu da wasu 'yan ta'adda a yankin Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja biyo bayan gano maɓoyar su da jami'an suka yi.

Majiyar mu ta Daily Trust ta ce 'yan ta'addan sun ɗauki mutane huɗu da suka fita yin aiki a gona a ranar Alhamis da ta gabata.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

Daga bisani 'yan ta'addan sun aiko mutum ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauke domin ya siyo musu man fetur.

Sojoji
Sojoji. Hoto: Leadership
Asali: UGC

Mutanen gari sun sanar da sojoji

Wakilin wata ƙungiyar matasa a yankin Jibril Allawa ya shaidawa majiyarmu cewa bayan da mutanen garin suka samu bayanai daga gurin wanda aka aiko, sai suka sanar da jami'an tsaro wanda su ka kai ɗauki cikin gaggawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin farmakin da jami'an tsaron sojin suka kai, mutane da dama da aka sace sun samu nasarar kuɓuta daga hannun masu garkuwar.

A cewarsa:

“Wasu gungun 'yan ta'adda ne a kan babura suka zo kusa da Allawa inda suka ɗauki wasu mutane huɗu da suke aiki a gona. Sannan suka aiko ɗaya daga cikinsu da kuɗi domin ya siyo musu mai da abin sha.”

Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan kwanton ɓauna

Kara karanta wannan

Tashin Hankalin Da Muka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru

Ya ƙara da cewar mutumin da aka aiko ya yi siyayyar ne ya sanar da al'umma halin da ake ciki inda su kuma suka sanar da jami'an tsaro na soji.

Jami'an sun tasa mutumin a gaba, suka yiwa 'yan ta'addan kwanton ɓauna sannan suka buɗe musu wuta.

'Yan ta'adda 30 sojoji suka kashe da kuma kuɓutar da mutane 20

Majiyar tamu ta ƙara da cewar anga wasu ƙasurguman 'yan ta'adda wato Kachalla Ali da Layee waɗanda suka addabi yankin Zamfara a wannan dajin.

Sojoji uku ne suka samu raunuka a yayin musayar wutar da ta faru tsakanin su da 'yan ta'addan.

The Sun ta wallafa cewa aƙalla 'yan ta'adda 30 ne sojojin suka yi nasarar kashewa a farmakin a yayin da wasu suka gudu da raunuka. Haka nan ma sojojin sunyi nasarar kuɓutar da aƙalla mutane 20 daga hannunsu.

'Yan ta'adda sun kashe magajin gari a Kaduna

Kara karanta wannan

Yadda Kasar Masar Ta Umarci Ɗaliban Najeriya Sama da 500 Su Koma Sudan Kan Halayyar Mutum 2

A wani labarin da Legit ta wallafa a kwanakin baya, kunji yadda wasu 'yan ta'adda suka kai hari a wani ƙauye a jihar Kaduna in da suka kashe magajin garin.

Mummunan lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Unguwar Liman da ke a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng