'Ya'yan Zamani: Wata Yarinya Ta Maka Mahaifinta a Kotu Kan Kokarin Yi Mata Auren Dole

'Ya'yan Zamani: Wata Yarinya Ta Maka Mahaifinta a Kotu Kan Kokarin Yi Mata Auren Dole

  • Wata ‘yarinya a Kaduna ta maka mahaifinta a kotu bisa zargin yi mata auren dole ga wanda ba ta so a zuciyarta
  • ‘Yarinyar mai suna Fatima ta ce tana da wanda take so a ranta inda ta nemi kotun da ta hana wannan auren
  • Mai shari’a, Mallam Isiyaku Abdulrahman ya tabbatar da cewa mahaifin nata yana da ‘yancin zaba wa ‘yarsa miji a shari’ance

Kaduna - Wata yarinya ta maka mahaifinta a wata kotu da ke zamanta a Kaduna inda ta roki kotun da ta hana auren dole da yake shirin yi mata.

Yarinyar mai suna Fatima, ‘yar shekara 20 ta bakin lauyanta Mallam Y.A Bulama ta ce tana da wanda take so.

kotun
Kotu, Hoto: Punch
Asali: Facebook

A cewar lauyan nata:

“Mahaifin yarinyar yana son ‘yarshi ta auri wani mutum a kauye cikin jihar Niger, a yanzu haka tana rayuwane a gidan ummarta saboda tilasta mata da mahifin ke son yi na aurar da ita ga wani a kauye.”

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Babban Sarki, Sun Sace Yayansa Da Jikoki 9 Da Wasu Mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa ‘yarinyar ba ta yi hakan ba ne don cin mutuncin mahaifinta, Punch.ng ta tattaro.

Ana shi bangaren, mahaifin ‘yarinyar ya ce iyayensa ne kafun rasuwarsu suka zaba mata miji, kuma dole ya bi umarninsu, kamar yadda rahotanni suka tattaro.

“Na aurar da ‘yata ta shida a kauye kuma suna zaune lafiya, mahaifiyarta ce take zuga ta.”

Bayanin mai shari'a

Mai shari’a, Mallam Isiyaku Abdulrahman ya tabbatar da cewa mahaifin yana da ‘yancin zaba wa ‘yarsa miji a shari’ance.

Ya kara da cewa auren dole ba abu mai kyau bane amma ya bai wa wanda ake karan shawara da ya yi hakuri da ‘yar tasa

“Kaine mahaifinta, ya kamata kayi mata addu’a don samun rayuwa mai kyau, in kana fushi da ita tabbas ba za ta ga abu mai kyau ba”.

Kara karanta wannan

Kallo ya koma sama: Yadda hotunan 'yar Najeriya a bikin nada sarkin Ingila suka bar jama'a baki bude

“Kabarta ta zabi wanda take so, in yana da addinin da tarbiya, sai ka barta ta aureshi”, in ji shi.

Ya kuma shawarci mai karar da ta kasance ‘ya mai bin umarnin iyayenta.

Kotun Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan jihar Osun

A wani labarin, kamar yadda Rahoton The Nation ya nuna cewa Kotun koli a Najeriya ta shirya yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya shigar gabanta yana kalubalantar nasarar Gwamna Ademola Adeleke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.