'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Karamar Hukuma a Taraba, Sun Sheke Dan Sandan da Ke Tare Dashi

'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Karamar Hukuma a Taraba, Sun Sheke Dan Sandan da Ke Tare Dashi

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun hallaka dan sandan da ke ba shugaban karamar hukumar Takum kariya a Taraba
  • Sun kuma sace shugaban karamar hukumarl Boyi Manja bayan da suka yi masa kwanton bauna a kan titi
  • Ya zuwa yanzu, rundunar 'yan sanda ta ce bata ci ta zama ba, tana bincike don gano wadanda suka yi barnar

Takum, jihar Taraba - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Takum ta jihar Taraba Boyi Manja tare da kashe dan sandan da ke bashi tsaro.

An yi garkuwa da Boyi ne a unguwar Kofai Ahmadu da ke kan hanyar Takum zuwa Wukari a ranar Lahadi 7a ga watan Mayu, Channels Tv ta ruwaito.

Wani na hannun daman shugaban da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an harbe mai ba abokin nasa kariya ne a lokacin da suke artabu da masu garkuwa da mutanen kafin su yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Mamayi Jami'an Tsaro Sun Buɗe Musu Wuta, An Rasa Rayuka

Yadda 'yan bindiga suka kashe shugaban karamar hukuma a Taraba
Jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

A cewarsa, shugaban da aka sacen, dan sandan da aka kashe, da direbansa sun baro Jalingo ne da nufin zuwa Takum amma suka gamu da 'yan bindiga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ‘yan sandan yankin suna ci gaba da sintiri a dajin yankin domin ganin an ceto shi, rahoton Leadership.

A cewar Abdullahi:

“Masu garkuwa da mutanen sun sanya shingen ne a lokacin da suka hango motarsa ta nufo, sai suka nemi direban ya bude bayan motar, ana cikin haka ne sai wadanda suka yi kwanton bauna suka bude wuta suka kashe dan sandansa da ke bashi tsaro.
“Kwamishanan ‘yan sanda ya bayar da umarnin a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da ceto wanda aka saen ba tare da bata lokaci ba."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Yankin Kudancin Kaduna, Sun Sace Matashiyar Budurwa

Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban karamar hukuma a Najeriya

A wani labarin, kunji yadda aka sace mataimakin shugaban karamar hukumar Isoko ta Arewa, Frank Esiwo Ozue a jihar Delta.

Ba wannan ne karon farko ba da ake sace 'yan siyasa a kasar nan duk da suna tafiya da masu basu kariya daga 'yan sanda, hakan ya sha faruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.