Zaben 2023: An Warware Gaskiya Kan Batun Obasanjo Ya Yi Hayar Lauyar da Ta Fi Kowa a Duniya Don Kare Peter Obi
- Gabanin fara shari’ar zabe a Najeriya, wasu rahotanni sun ce tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi hayar lauya ’yar kasar Rasha don wakiltar Peter Obi na Labour a kotu
- Sai dai, hadimin Obasanjo, Kahinde Akinyemi ya karyata jita-jitan da ake yadawa, inda yace mai gidansa bai dauki wata lauya don wakiltar dan takarar shugaban kasan na Labour ba
- Shari’ar da za a yi kan zabe za ta yi magana da kuma duba mai gaskiya ne tsakanin Tinubu, Obi da Atiku game da zaben shugaban kasa na bana
Gabanin fara shari’a a kotun zabe game da kararrakin kalubalantar samakakon zabe, an ce Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya ya yiwa Peter Obi alheri.
An yada jita-jita cewa, Obasanjo ya yi hayar wata lauya ‘yar kasar Rasha domin wakiltar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.
A cewar jita-jitar da ake yadawa:
“Obasanjo ya dauko wata fitacciyar lauya a duniya ‘yar kasar Rasha “Natalia Veselnitskaya” don kare Peter Obi gabanin zaman kotu kan zaben shugaban kasa.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani mai suna @SpecialConvenant a Twitter ya ce:
“A cewar rahotanni, ana mata kallon lauya mafi hadari a duniya da bata faduwa ba a gaban kotu.”
Wani kuma mai suna @Classycrystale1 cewa ya yi, Natalia lauya ce ta kusa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Obasanjo bai daukar wa Obi lauya ba
Da yake martani, hadimin Obasanjo, Kahinde Akinyemi ya bayyana cewa, mai gidansa bai dauko wata lauya daga Rasha mai suna Nataliya Veselnitskaya ba don wakiltar Peter Obi.
Ya kuma yi karin haske da cewa, akwai bukatar ‘yan Najeriya suke bin diddigi da kuma tace gaskiya a lamari irin wannan, rahoton ICIR.
A cewar Kahinde:
“Jita-jitace wacce ba a tabbatar ba, kuma bata da alaka da Obasanjo. Bugu da kari, bata fito daga majiya mai tushe ba."
Daga baya, binciken da Legit.ng ta yi ta gano cewa, babu wata kafar yada labarai tsayayya da ta wallafa labari kan dauko Natalia daga Rasha don Peter Obi.
A tun farko, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanmar a watan Faburairun da ya gabata cikin shekarar nan.
Asali: Legit.ng