Na Tuba: Budurwar Da Ke Tallan Kanta Da Hotunan Batsa Ta Tuba, Ta Mika Rayuwarta Ga Addini
- Wata budurwar da a yanzu ta rungumi tafiyar addinin kirista sau da kafa ta fadi yadda tasirin annabi Isa ya sauya rayuwarta
- Budurwar ta ce, a baya takan yada hotunanta tsirara a kafar sada zumunta don kawai jan hankalin maza, amma yanzu ta sauya
- Ta alakanta sauyin da ta samu a rayuwarta da yadda tasirin almasihu yake a lokacin da ta karbi tafiyarsa sau da kafa
Wata budurwa da a baya take tallan kanta a kafar sada zumunta don jama’a su gani ta ce yanzu ta sauya rayuwarta.
A cewar budurwar, rayuwarta ta sauya tun bayan da ta rungumi tafiyar Annabi Isa a addinin kirista.
A cewarta, a baya takan yada hotunanta da ke nuna tsiraici, inda take nuna sassan jikinta da bai kamata a gani ba don neman jan hankalin maza.
Yanzu ta tuba, ta daina komai irin wannan
Amma a yanzu, ta ce ta karbi tafiyar addinin kirista sau da kafa, ta kuma sauya rayuwarta zuwa mutumiyar kirki mai bin annabi Isa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A shafinta na Twitter mai suna @bornagainsteph, ta ce:
“Na kasance ina nuna jiki na don jan hankalin jama’a. Ban saka komai sai gajeren wando, yankakken riga ta sama da kuma matsattsun kaya.
“Amma Yesu ya cece ni kuma ya sauya ni! Shashanci, yada tsiraici da alfasha ba hanya mai kyau bace ga mata. Kamun kai, mutunta kai da daraja kai sune. Nagode Yesu!
“Ina ba da shaida! Shekarata 25 kuma na tsira ne ina da shekaru 24. Akwai ‘yan mata da yawa irina a yanzu a ko ina da ke bukatar irin wannan shaida.
“Ina kawai yada gaskiyata ce game da Yesu da ya sauya ni. Ba a rene ni a coci ba ko kada; Yesu zai iya ceton kowa.”
“Turo Mun N400k Ko Na Rabu Da Kai”: Matashiya Ta Yi Barazana Ga Saurayinta, Hoton Hirarsu Ya Bayyana
Wannan dai ra’ayi ne na wannan budurwar, kuma addini da fahimtarsa yakini, ba lallai ya zama gaskiya ga kowa ba.
Martanin jama’a
@AngelinaTamezTX:
“Kamun kai na da matukar kyau!!”
@tmmdaytontexas:
“Ubangiji ya albarkaci imaninki. Alamu sun nuna kika da aiki da yawa a tsohuwar rayuwarki. Ba tare da tunin imani ba a kowacce rana, ba zai yiwu ki share kazantar baya ba da ke zaune a cikin rai a rayuwa mai cike da kawa.”
Asali: Legit.ng