“Na Rantse Zan Yi Mulki da Adalci”: Sarki Charles III Yayi Magana Bayan Nada Shi Sarauta
- A ranar Asabar 6 ga watan Mayu ne Burtaniya ta nada sarki Charles II watanni takwas bayan hawansa sarauta biyo bayan mutuwar mahaifiyarsa sarauniya Elizabeth II a watan Satumba
- Sarki Charles ya yi rantsuwa da Allah cewa, zai yi mulkinsa da adalci da tausayi, kuma zai yi aiki da daidai da mazhabobin addinin kirista na cocunan Anglican na Ingila da kuma Presbyterian na Scotland
- Da aka tabbatar da nada shi, sarkin na Ingila ya ce zai kiyaye martabar masarautar da kuma bin kadun dukkan addinai
Landan, Burtaniya - Sarki Charles II a zama cikakken sarkin Ingila a yau Asabar 6 ga watan Mayu, inda ya rantse da Allah wajen yiwa al’ummarsa adalci kuma zai yi mulki da tausayi.
Ya kuma bayyana cewa, zai riki akidu da mazhabobin addinin kirista na cocunan Anglican na Ingila da kuma Presbyterian na Scotland.
Legit.ng ta tattaro cewa, a karon farko a tarihin burtaniya, sarkin ya yi addu’a da neman albarkar dukkan addinai da mazhabobin addinai.
Da yake jawabi a lokacin rantsar dashi a Westminister Abbey, ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Na rantse zan mulki mutane da adalci da tausayi, kuma zan yi riko da mazhabar cocin Anglican na Ingila da kuma na Presbyterian na Scotland.”
Mafi daraja a bikin, shine sanyawar albarkar babban Archbishop na Canterbury, Justin Welby, inda ya wanke hanni, kirji da kan sarkin da mai na musamman mai barka.
Yadda sarki Charles ya zama sabon sarkin Ingila
Bayan mutuwar sarauniya Elizabeth II a watan Satumban 2022, an alanta danta na fari, Charles a matsayinw anda zai dare kujerarta; ya zama sarki Charles III.
Sabon sarkin ya kasance yariman Wales, matsayin da ake ba yarima mai jiran gado a masarautar Ingila.
“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtaniya Ta Ba Shi Mafaka
Mahaifiyar tasa ta rasu ne tana shekaru 96 a gidan duwatsu na Balmoral Castle da ke Aberdeenshire a watan Satumban bara, inda duniya ta shiga jimami.
Mata ‘yar Najeriya ta wanke taro da shiga mai kyau
A wani labarin, kun ga hotunan wata mata da ta wanke taro da kayan al’adar ‘yan Najeriya a bikin nada sarki Charles.
Wannan lamari ya ba da mamaki, mutane da yawa sun bayyana yabo da jin dadinsu kan yadda ta wakilci ‘yan kasar nan.
An ganta sanye da sutura irinta Yarbawa, lamarin da yasa wasu ke ganin ta yi hakan ne don wakiltar ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng