“Ina Ji Kamar Laifina Ne”: Sonia Ekweremadu Ta Magantu Kan Daure Iyayenta Da Aka Yi a Bidiyo

“Ina Ji Kamar Laifina Ne”: Sonia Ekweremadu Ta Magantu Kan Daure Iyayenta Da Aka Yi a Bidiyo

  • Sonia Ekweremadu, diyar Ike da Beatrice Ekweremadu, ta magantu kan hukuncin da aka yankewa iyayenta
  • A safiyar Juma'a, 5 ga watan Mayu, kotun majistare na Birtaniya ta yankewa Sanata Ike da Beatrice Ekweremadu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kurkuku
  • Sonia mai shekaru 25, wacce ke fama da cutar koda ta ce hukuncin kotun ya yi mata ciwo

Bayan yanke wa Sanata Ike Ekweremadu, matarsa Beatrice da wani likita hukuncin dauri, Sonia, diyarsu mai shekaru 25 ta magantu kan halin da iyayenta ke ciki.

A ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu ne wata kotun majistare a Birtaniya ta yankewa Sanata Ekweremadu daurin shekaru 10 a gidan yari yayin da matarsa Beatrice ta samu daurin shekaru hudu bayan kotun ta same su da laifin safarar sassan jikin mutum.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa Ekweremadu Shekaru 10 A Gidan Yari Kan Safarar Sassan Jikin Bil Adama

An dai same su da laifin shigo da wani dan shekaru 22 daga Najeriya ba bisa ka'ida ba don sakawa Sonia kodarsa.

Ike Ekweremadu, diyarsa da matarsa
“Ina Ji Kamar Laifina Ne”: Sonia Ekweremadu Ta Magantu Kan Daure Iyayenta Da Aka Yi a Bidiyo Hoto: BBC Pidgin, Ike Ekweremadu and Adrian Dennis/AFP
Asali: UGC

A yayin hirarsu da BBC Pidgin jim kadan bayan yankewa mahaifinta hukunci, Sonia ta bayyana yadda ta shiga wani hali da karayar zuciya bayan tura iyayenta gidan yari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta bayyana cewa babu adalci a hukuncin yayin da ta gaggauta bayyana cewa dalilinta na tattare da son kai a matsayinta na diyarsu kuma cewa za ta goyi bayan iyayenta ne a kowani yanayi.

Da aka tambayeta game da matsayinta kan wannan hukuncin, Sonia ta ce:

"Abun bakin ciki ne. Yana da matukar nauyi daukar wannan a kaina. Na fahimci hukuncin. Ni a karan kaina, ban yarda da shi ba; wannan tunanine na son kai a matsayina na diyarsu, kuma zan shakka babu bayan iyayena zan bi.

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Bacci Ni Kadai Ba”: Uwa Ta Bude Kofar Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta, Mutane Sun Bata Shawara

"Sai dai kuma, doka ta yi halinta, kuma dole mu ci gaba da rayuwa a matsayinmu na iyali."

Kotun Birtaniya ta daure Ekweremadu na shekaru 10

A baya mun ji cewa wata kotun majistare na Birtaniya ta yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu hukuncin daurin shekaru 9 da watanni takwas a gidan yari bisa laifin safarar sassan jikin dan Adam.

Hakazalika, kotun ta kuma yanke ma matar shi Beatrice Ekweremadu hukuncin shekaru hudu da wata shida a gidan gyara hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel