Za a Zauna a Cikin Duhu, Gwamnatin Tarayya Ta Yanke Wuta Daga Kamfanonin DisCos

Za a Zauna a Cikin Duhu, Gwamnatin Tarayya Ta Yanke Wuta Daga Kamfanonin DisCos

  • Gwamnatin tarayya ta shiga datse kamfanonin da ke raba wuta daga babban layin lantarkin kasar
  • Kamfanin TCN ya na kukan DisCos da GenCos sun gagara sauke nauyin bashin da ake binsu
  • Abin da hakan zai jawo shi ne Bayin Allah za su koma rayuwa a duhu a wurare dabam-dabam

Abuja - Idan abubuwa ba su canza ba, miliyoyin mutane za su koma rayuwa cikin duhu domin gwamnatin tarayya ta fara katse wutar lantarki.

Punch ta kawo rahoto cewa gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin TCN sun soma yanke kamfanonin DisCos daga babban garken lantarkin kasa.

Bincike ya nuna hakan ya zo ne bayan gwamnati ta sanar da wadannan kamfanoni da ke raba wuta zuwa ga mutane cewa za a datse su daga layi.

Wani bangaren TCN da ke kula da ‘yan kasuwa ya rubuta takarda zuwa DisCos da kamfanonin GenCos masu samar da wutar lantarki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Manyan Fastoci 100 a Najeriya Sun Yi Barazanar Tofa Tsinuwa Ga Masu Son Kafa Gwamnatin Wucin Gadi

Ba a samun wutar lantarki sosai

Rahoton ya ce hukuma ta fadawa kamfanonin rashin biyan bashin da yake kan wuyansu, zai jawo su daina samun rabon wuta daga babban layi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun lokacin abubuwa suka tabarbare, mafi yawan mutane su ka koma kukan rashin wuta.

Lantarki
Tashar wutar lantarki Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Jerin wadanda abin ya shafa

Kamfanonin samarwa da raba lantarki da abin ya shafa sun hada da AEDC, BEDC, EEDC da ke rabawa mutane wuta a yankin Abuja, Benuwai da Enugu.

Pulse ta ce wadanda ake bi bashi sun hada da IEDC, IE, JEDC, KEDCO, PHEDC, APL, da kamfanin da yake bada lantarki ga kamfanin karafuna na Ajaokuta.

Kamfanonin GenCos da matakin ya shafa sun hada da tashohin NDPHC da kamfanin Paras Energy.

Kowa yana kuka da kowa

Mai magana da yawun kungiyar kamfanonin raba wutar lantarki, Sunday Oduntan bai yarda ya yi magana a kan batun ba a lokacin da aka tuntube shi.

Kara karanta wannan

To fah: Tinubu ya tafi ganawa da gwamnan PDP, kwamitin NWC na APC ya shiga ganawa

Wasu kamfanoni sun ce bashin ya taru masu ne saboda jama'a ba su biyan kudin wuta, a gefe guda jama'a su na kukan ana lafta masu kudi da yawa.

Darektan sashen MO a kamfanin TCN, Eddy Eje ya fitar da jawabi inda ya bukaci DisCos su biya bashinsu bayan Minista ya sa baki an dawo da wuta.

A watannin da suka wuce, an ji labari kamfanin lantarki na Najeriya ya yi ta fama da ma’aikatan wutar lantarki, yana rokonsu kan shirin shiga yajin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng