Sojoji Sun Gargaɗi 'Yan Siyasar da Ke Shirin Kawo Cikas Ga Rantsar da Shugaban Ƙasa
- Rundunar Tsaron soji ta ja kunnen duk masu yinƙurin kawo cikas dangane da bikin rantsarwar
- Rundunar Sojin ta ce jami'an ta a shirye suke su ɗauki dukkan matakin da ya dace
- Rundunar ta kuma sha alwashin binciko duk masu kitsa ƙulle-ƙullen
Rundunar sojin Najeriya ta gargaɗi 'yan siyasar da ke yinƙurin kawo cikas kan batun rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Ahmad Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu akan cewa su cire tunanin hakan daga ran su.
Hukumar ta ce jami'an ta a shirye suke don daƙile duk wani yinƙuri na kawo matsala a cikin ƙasa gabanin, ko lokacin, ko kuma bayan bikin rantsar da sabuwar gwamnati da zai gudana a ƙarshen watan nan da mu ke ciki.
Daraktan watsa labarai na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janaral Musa Ɗanmadami ne ya fitar da sanarwar gargaɗin a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga 'yan jarida jim kaɗan bayan gama taron manema labarai na rundunar kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Tinubu, Atiku Ko Obi? Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Alfarma 1 Wurin Yan Najeriya Kan Shari'ar Zaben 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zamu binciko duk wasu masu ƙulla maƙarƙashiya
Ko a sati biyu da suka gabata nan baya, Punch ta wallafa labarin cewa rundunar sojin ta sha alwashin bin diddiƙi gami da binciko duk wasu masu yinƙurin kawo hargitsi a cikin ƙasa a yayin bukin miƙa mulkin.
Da ya ke amsa wasu daga cikin tambayoyin a wajen taron da ya gudana ranar Alhamis, Ɗanmadami ya ce bai ga wani dalilin da zai sanya ace rantsuwar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba za ta yiwu ba.
Ɗanmadami ya ce:
“A iya sanina da harkokin tsaron cikin gida, jami'an hukumar 'yan sanda sune a gaba. Rundunar soji da sauran nau'uka na jami'an tsaro na taimaka wa ne dai kawai. Ina son ƙara jaddada muku cewa muna nan a cikin shiri domin tabbatar da cewa wani mummunan al'amari bai faru ba.”
“Akan ɗauki matakin gaggawa akan batun barazana ga tsaro da zaman lafiya. An riga da an gudanar da zaɓuka kuma an gama. Haka nan ma zaɓen shugaban ƙasa an riga da an sanar da wanda yayi nasara.”
Za a yi taron rantsarwar lafiya a tashi lafiya
Ya kuma ƙara da cewar akwai nau'o'in jami'an tsaro daban-daban a yayin da za a gudanar da bukukuwan rantsarwar duk domin dai a tabbatar da cewa an yi komai an gama lafiya.
Saboda haka ya ce bai ga wani dalili da zai sa a tsammaci wata matsala ba a yayin rantsarwar. Ya jaddada cewa za a gudanar da bukin lafiya a kuma tashi lafiya. Ya kuma ce ba za su yi ƙasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da tsaro a kowane lungo da saƙo na ƙasar nan.
Ni ba mai laifi ba ne, tunda kotu ba ta ayyana hakan ba
A wani labarin na daban kuma, Alhassan Ado Doguwa, ɗan majalisar dokoki da ke wakiltar Tudun Wada da Doguwa ya ce shi fa ba mai laifi ba ne har sai dai idan kotu ce ta ayyana shi a matsayin mai laifin.
Ya bayyana hakan ne a zauren majalisar dokokin a lokacin da yake ƙaddamar da yaƙin neman kujerar kakakin majalisar da yanzu haka take da manema aƙalla guda 7.
Asali: Legit.ng