Kwamitin Ayyukan APC Ya Shiga Ganawar Sirri a Yau Laraba Kan Matsalolin Jam’iyyar
- Jam'iyyar APC ta zauna don warwarewa da duba ga wasu matsalolin da ke gabanta bayan kammala zaben shugaban kasa
- Jam'iyyar za ta yi duba ga abubuwa da yawa, duk da a hukumance ba a bayyana gaskiyar dalilin zaman ba
- A bangare guda, zababben shugaban kasa Tinubu ya shilla jihar Ribas domin ganawa da gwamna Nyesom Wike
FCT, Abuja - Kwmaitin ayyuka na jam’iyyar APC ya shiga wani muhimmin taro a yanzu haka a sakateriyar jam’iyyar da ke babban birnin tarayya Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana dalilin ganawar ba a hukumance, The Nation ta tattaro cewa, ganawar na da nasaba da yin duba ga zabukan da aka kammala a gwamnan nan.
Hakazalika, ganawar za ta yi duba ga rahotannin bincike kan zaben da kuma batutuwa da suka shafi rahotannin kudi da za a kai wa kwamitin NEC na APC a nan gaba.
A bangare guda, rahoton da muka samo ya ce, zaman zai yi duba ga batun mika kujerun shugabancin majalisar kasar nan zuwa yankunan da suka dace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran batutuwan da za a tattauna a kansu
A cewar jaridar, zaman zai tattara batun da ya dace game da shugabancin majalisar ta 10 tare da mika wa Buhari da Tinubu gabanin rantsar da majalisar a watan Yuni, Within Nigeria ta tattaro.
Bugu da kari, a jerin abubuwan da za a tattauna akai akwai batun da mataimakin shugaban APC, Salihu Muhammadu Lukman ya gabatar da kuma matakin doka game da zargin shugaban APC da mataimakinsa sun saba ka’idar jam’iyyar.
Idan baku manta ba, lamurra sun yi tsami a APC a makon jiya yayin da mai ba APC shawari kan harkokin shari’a, Ahmad Usman El-Marzu ya ba da shawarin a kori Lukman bisa kai jam’iyyar kara gaban kotu.
A halin da ake ciki, ganawar da aka yi yau dai na faruwa ne karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, sanata Abdullahi Adamu da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar 18 daga kwamitin NEC mai mambobi 24.
Tinubu ya dura a Ribas
A bangare guda, Bola Ahmad Tinubu ya dura a jihar Ribas domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamna Wike ya yi.
Tinubu zai shafe kwanaki biyu ne a jihar, inda zai kaddamar da wasu manyan ayyukan da gwamnan ya yi a mulkinsa.
Asali: Legit.ng