"Ina Da Mata 4 Da 'Ya'ya 28": Hujjar Ni Zan Yi Nasara A Shugabancin Majalisar Wakilai, In Ji Doguwa

"Ina Da Mata 4 Da 'Ya'ya 28": Hujjar Ni Zan Yi Nasara A Shugabancin Majalisar Wakilai, In Ji Doguwa

  • Alhassan Ado Doguwa ya bayyana kwarin gwiwarsa na zama kakakin majalisar wakilai ta kasa anan gaba
  • A cewarsa, bai da fushi kamar yadda wasu ke tsammani, kawai dai mutane basu fahimci waye shi bane
  • Doguwa ya ce, ya auri mata hudu da yake rayuwa dasu yanzu, yana da ‘ya’ya 28 amma bai taba yin saki ba

FCT, Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya bayyana kwarin gwiwar zama shugaban majalisa ta 10, Punch ta ruwaito.

Ya kuma soki wadanda ke yi masa gani-gani, inda yace shi shugaba ne da ya iya rike mata hudu da ‘ya’ya 28, don haka yana da yakinin nasara.

Kamalan Doguwa na zuwa ne a matsayin martani ga masu cewa bai cancanci gaje kujerar shugaban na yanzu ba, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki

Ado Doguwa ya fadi sirrin nasararsa
Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye a majalisa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jama’a basu faminci waye Ado Doguwa ba, cewar Doguwa

Da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba 3 Mayu, 2023, ya ce wadanda ke son bata shi basu ma fahimci waye shi ba, The Times ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Ga wadanda ke min kallon mutum mai yawan fushi, basu san Ado Doguwa ba, mutumin da ke da mata hudu da ‘ya’ya 28.
“Ban taba saki ba. Wannan ya nuna ina da abin da ake bukata na zama kakaki a nan gaba. Zan zama shimfida ga ‘yan Najeriya su taka ko kuma wuce a kai.”

A matsayina na dan siyasa, kowane mutum dabba ne na siyasa. Kuma dole za a same shi da wani abin da ba daidai ba. Batun fushi kuma fahimta ce. Abin da wani zai ce fushi ne wani sabanin haka zai gani.

Kara karanta wannan

"Ba Ni Da Laifa Sai Kotu Ta Tabbatar": Tuhumar Kisa Da Ake Min Ba Zai Hana Ni Neman Mukami Ba, Ado Doguwa

Na ba da gudunmawa ga al’umma ta a majalisa, inji Doguwa

Ya kuma bayyana yadda ya ba da gudunmawa a aikin majalisa tun 1992 da kuma yadda yadda ya ba al’umma gudunmawa.

Hakazalika, ya yi bayani game da dambarwar da yake fuskanta a gaban kotu game da rikicin da ya faru a Kano na siyasa da ake alanta shi da ‘yan tsaginsa da shi kansa.

A wani labarin, kunji yadda aka kama Ado Doguwa a jihar Kano bisa zarginsa da hannu a kisan wasu mutane da kuma raunata wasu a zaben da aka gudanar a mazabarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.