Bidiyon Lokacin da Bola Tinubu Ya Sauka a Jihar Ribas Ya Dauki Hankalin Jama’a
- Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Ribas ta Nyeson Wike na jam’iyyar PDP
- Jam’iyyar APC ta ce ba da yawunta ba Tinubu zai kai ziyara jihar Ribas saboda jiha ce ta PDP shi kuma dan APC
- Ba sabon abu bane a Najeriya a samu rashin jituwa a tsakanin mambobin jam’iyyun siyasa da masu bin bayansu
Wani bidiyon da aka yada ya nuna lokacin da zababben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ke sauka daga jirgi yayin da ya kai ziyara jihar Ribas.
Wannan na zuwa ne a wata ziyarar da shugaban ya kai jihar don hakartar tarukan kaddamar da ayyukan da gwamnan PDP, Nyesom Wike ya yi a jihar.
A tun farko, gwamnan ya gayyaci Tinubu zuwa jiharsa tare da ba da hutu a jihar a ziyarar da Tinubu zai kai ta kwana biyu a jihar.
An ruwaito cewa, Tinubu zai kaddamar wasu manyan ayyuka a jihar, ciki har da gadar sama da gwamnan ya yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tinubu ya sauka a jirgi a Ribas
Duk da cewa jam’iyyar APC ta nesanta kanta da yunkurin Tinubu na zuwa jihar Ribas, an ga sabon shugaban kasan a jihar lokacin da yake sauka daga jirgin sama.
Bidiyon da muka gani ya nuna cewa, Tinubu ya sauka a jihar ne tare da wasu jiga-jigan na hannun damansa da ya saba tafiya tare dasu.
Hakazalika, akwai dandazon jama’ar da suka taru domin tarbar zababben shugaban kasan a daidai lokacin da ya sauka.
An ji muryar jama’ar da ke kirari da ambatar sunan ‘Jagaban’, inda suke marabtarsa da nuna kauna gare shi.
Makaho ne kadai zai ce Tinubu ya lashe zabe
A wani labarin, kun ji yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya bayyana matsayarsa game da zaben shugaban kasan da aka yi a wannan shekarar.
A cewar Labour da dan takararta, an yi magudi a zaben shugaban kasan da ya gudana a kasar, jam’iyyar ta fadi dalilinta na fadin wannan maganar.
A tun farko, Peter Obi ya tafi kotu don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa, ya ce makaho ne kadai zai ce ba yi magudi a zaben bana ba.
Asali: Legit.ng