Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wata Budurwa a Kudancin Kaduna

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wata Budurwa a Kudancin Kaduna

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da wata matashiyar budurwa a yankin Fadan Ikulu da ke masarautar Ikulu, karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna
  • Masu garkuwa da mutanen sun kai farmaki ne da tsakar dare sannan suka dunga harbi don tsorata jama'a kafin suka sace budurwar
  • Uwar yarinyar ta yi kira ga hukumomin tsaro a kan su gano inda diyarta take yayin da tace har yanzu maharan basu kirata ba

Kaduna - Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wata budurwa mai suna Benifica Haruna a safiyar ranar Talata a yankin Fadan Ikulu da ke masarautar Ikulu, karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.

Masu garkuwa da mutanen sun farmaki yankin da misalin karfe 12:00 na tsakar dare sannan suka fara harbi a iska don tsorata mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Zariya, Sun Kashe Mutum 2 Da Sace Wasu 4

Jami'an yan sanda
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sace Wata Budurwa a Kudancin Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru, mahaifiyar yarinyar ta magantu

Da take tabbatar da lamarin ga jaridar Daily Trust, mahaifiyar budurwar da aka sace, Sarauniya Ikulu ta ce diyarta na cikin dakinta lokacin da suka ji karar harbi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewar:

"Ta kirani kan na je na boye a wani wuri a gidan ba tare da sanin cewa mu suke hari ba."

Masu garkuwa da mutanen wadanda suka zo a cikin motoci da babura sun shafe kusan awa biyu suna aiki ba tare da jami'an tsaro sun shiga lamarin ba.

Don haka take kira ga hukumomin tsaro da su binciki lamarin sannan su binciko inda diyarta take.

Matar ta bayyana cewa ba ta samu kowani bayani kan diyarta ba daga bangaren wadanda suka sace ta ba.

Ba a ji daga bangaren yan sanda ba

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Cika Hannu Da Yan Sara-Suka 98 a Wata Jihar Arewa

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige bai amsa wayansa ba don jin ta bakinsa a kan lamarin.

Yan bindiga sun kai hari yankin Zariya, sun kashe mutane 2 tare da sace wasu 5

A wani labarin kuma, wasu yan bindiga sun farmaki yankin Zariya a jihar Kaduna inda suka halaka wasu mutane biyu da ke kan hanyarsu ta wucewa.

Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane hudu a yankin Kofar Kona da ke garin Zariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng