Mayu Sun Mika Wata Kwakwarar Bukata 1 Daga Yan Najeriya Gabanin Rantsar Da Tinubu
- Ƙungiyar fararren mayu ta tabbatar da goyon bayan ta ga Asiwaju Bola Tinubu har zuwa lokacin rantsuwa
- Sun Buƙaci 'yan Najeriya su taya zaɓaɓɓen shugaban da addu'ar samun nasarar cika alkawuran da ya dauka
- Ƙungiyar matsafan ta gargaɗi masu son kawo cikas dangane da batun rantsar da sabon shugaban
Ƙungiyar fararren mayu da matsafa ta ƙasa ta buƙaci 'yan Najeriya da su yi wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu'a gabanin rantsar da shi da za a yi a ranar 29 ga watan Mayun da muke ciki.
Sun bayyana cewa babu abinda Tinubu yake buƙata a yanzu fiye da addu'ar 'yan Najeriya wajen ganin ya samu ikon cika alƙawuran da ya ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe.
Majiyar mu ta Legit ng ta ruwaito hakan daga bakin mai magana da yawun ƙungiyar wato Okhue Obo, wanda ya ƙara jaddada ma Tinubu goyon bayan su daga yanzu har zuwa lokacin da zai karɓi mulki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka zalika, ƙungiyar ta gargaɗi batagarin 'yan siyasa akan duk wata maƙarƙashiya da suke ƙoƙarin shirya wa don ganin sun kawo tasgaro akan rantsar da zaɓaɓɓen shugaban.
Muna yi ma Tinubu barka da dawowa gida Najeriya. Zaku iya tuna cewa Tinubu ne ya lashe zaɓen da muka gudanar a tsakanin mu wata biyu gabanin babban zaɓen da ya gabata a 25 ga watan Fabrairu.
Kada Tinubu ya ɗaga hankalin shi
Ƙungiyar ta mayu da matsafa ta ce ta fahimci cewa akwai wasu dake yunƙurin kawo yamutsi a cikin ƙasa don ganin sun kawo cikas game da batun rantsar da Tinubu.
Sun bayyana cewa ko kaɗan kada yaji wani abu a ran shi domin kuwa yanzu haka suna kan aikin magance duk wasu tsubbace-tsubbace da aka yi mishi a Abuja, kuma babu wani abu da zai yi tasiri a kan shi, kamar yadda Tribune ta wallafa.
Rikicin Sudan: An Hana Daruwan Dalibai 'Yan Najeriya Tsallakawa Zuwa Kasar Egypt, Dalilai Sun Bayyana
Babu abinda Tinubu yake buƙata daga 'yan Najeriya a yanzu fiye da addu'ar samun lafiya da tsawancin kwana ta yadda zai samu damar cikar alƙawuran shi na inganta rayuwar al'umma. inji shi.
Motar da ke jigilar ɗalibai ta kama da wuta
A wani labarin na daban kuma, ɗaya daga cikin motocin da ke jigilar ɗaliban Najeriya daga Sudan zuwa bakin ruwa domin fitar dasu daga ƙasar ta gamu da ibtila'in kamawa da wuta.
Ana dai ƙoƙarin ganin an kwashe ɗaliban daga babban birnin ƙasar wato Khartoum wanda yake fama da yaƙi tsakanin gwamnati da 'yan tawayen dake fafutukar kifar da gwamnati zuwa tashar jirgin ruwa inda daga nan za su haura zuwa ƙasar Saudiyya.
Tuni dai ƙasashe da dama suka yi nasarar kwashe 'yan ƙasar su daga yankin da ke fama da rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Asali: Legit.ng