Gwamna Soludo Ya Yi Barazanar Rage Albashin Ma'aikata Masu Fashin Zuwa Aiki
- Gwamna Soludo na jihar Anambra ya yi barazanar rage albashin ma'aikata masu ƙin zuwa wurin aiki a ranakun dokar zaman gida
- Yan ta'adda sun saka dokar zaman gida a kowace ranar Litinin, lamarin da ya jawo mazauna jihar ke fargabar gudanar da harkokinsu
- Sai dai gwamnan ya ce ba zai lamurci haka ba domin abun ya fara zama uzurin rashin zuwa aiki a jihar
Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya yi barazanar rage albashin ma'aikatan da basu zuwa wurin aiki a ranakun dokar zaman gida a jihar.
Soludo ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga dandazon ma'aikatan da suka halarci bikin ranar ma'aikata wanda ya gudana a Dakta Alex Ekwueme Square, Awka, babban birnin Anambra ranar Litinin.
A cewar gwamnan, dokar zaman gida ranar Litinin ta zama uzuri a wurin ma'aikata na daina zuwa wurin aiki a duk ranakun Litinin na kowane mako kuma hakan ba zata saɓu ba.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a baya-bayan nan gwamna Soludo ya ƙara wa ma'aikata albashi da kaso 10% a jihar wacce ke shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ina aka samu dokar zaman gida ranar Litinin?
Jihar Anambra na ɗaya daga cikin jihohin kudu maso gabas, waɗanda ke fama da hare-haren 'yan bindigan da ba'a sani ba da kuma ƙungiyar 'yan aware watau IPOB.
Ƙungiyar IPOB, wacce gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci, ita ake zargi da kakaba dokar zaman gida a kowace Litinin.
Da yawan mazauna jihar kama daga yan kasuwa, masu saye da sayarwa da ma'aikatan gwamnati na fargabar fita zuwa wurin ayyukansu saboda abinda ka iya zuwa ya dawo.
Wannan ne ya sa ma'aikatan gwamnatin jihar Anambra ke ba da uzurin dokar zaman gida suna kauracewa fita domin tseratar da rayuwarsu, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Shin kun san me ake nufi da ranar 1 ga watan Mayu?
A wani labarin kuma Muhimman Abubuwa Bakwai Game Da Ranar 1 Ga Watan Mayu Na Kowace Shekara
A kowace ranar 1 ga watan Mayu, ake bikin ranar ma'aikata ta duniya domin nuna irin gudummuwar da ma'aikata ke bayarwa da sadaukarwarsu.
Legit.ng Hausa ta haɗo muku wasu muhimman abubuwa da ya dace ku sani game da wannan rana.
Asali: Legit.ng