Gwamna Ya Fayyace Halin da Ake Ciki, Ya Ce Biyan Albashi Zai Iya Gagara Nan da Wata 1
- Godwin Obaseki ya nunawa ma’aikata su shirya ganin tsadar rayuwa da kara shiga mawuyacin hali
- Da ya halarci bikin ranar ma’aikatan Najeriya, Gwamnan ya nuna san an yi da gaske wajen samun albashi
- Gwamna Obaseki ya ce a yanzu ya zama tilas ga gwamnatin Najeriya ta daina biyan tallafin man fetur
Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ce watakila gwamnatin tarayya ba za ta iya biyan ma’aikata albashinsu bayan watan Yuni mai zuwa ba.
A ranar Litinin, The Cable ta rahoto Gwamna Godwin Obaseki yana cewa dole a janye tallafin man fetur ko ayi ta buga kudi idan ana so a biya albashi.
Mai girma Godwin Obaseki ya yi wannan ikirari ne a lokacin bikin ranar ma’aikata da ya gudana a babban birnin jihar Edo na Benin a farkon makon nan.
Gwamnan na Edo ya ce nan da kowane lokaci, ma’aikata za su iya shiga mawuyancin hali a kasar, don haka ya fada masu su shirya tun wuri.
Jawabin Gwamna Godwin Obaseki
“Ikon Allah kurum zai sa gwamnatin tarayya da na jihohi su iya biyan albashi bayan Yunin shekarar nan ba tare da an koma buga ko janye tallafin fetur ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kowane daga cikin wannan mataki aka dauka zai kara jefa al’umma cikin halin kunci da wahala, musamman ma’aikata.
Dole mu tabbata ba ma’aikata kurum aka bari a mawuyacin halin da za a shiga a dalilin daukar matakan da suka zama dole ba.
Ya zama wajibi ma’aikata su tashi tsaye, su tabbata sun goyi bayan janye tallafin man fetur.
- Godwin Obaseki
An rahoto Obaseki ya ce lokaci ya yi da ma’aikata za su nemi gwamnati ta yi gaskiya, ta fito da komai keke-da-keke idan an dauki irin wadannan matakai.
An ga SSG da manya jiha a taro
Kamar yadda This Day ta fitar da rahotonta, mataimakin Gwamna, Philip Shaibu da sakataren gwamnatin Edo, Osarodion Ogie sun halarci taron da aka yi.
An hangi Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Edo, shugaban majalisar dokoki, babban Alkalin jiha da shugaban ma’aikatan fadar gwamna wajen bikin.
Nasarori da aka samu a shekaru 8
Daga karshen Mayun 2015 zuwa shekarar nan ta 2023 da ake ciki, an ji labarin irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawowa ‘Yan Najeriya.
Femi Adesina ya ce NIS mai kula da shige da fice ta fadada ofisoshinta, ta kawo e-fasfo, sannan Hukumar NDLEA ta dage a yakar safarar miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng