Musayar Kalamai Tsakanin APC da PDP Na Kara Kamari Game Sakamakon Zaben 2023
- Watanni biyu bayan kamala zaben shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour na ci gaba da cewa su suka lashe zaben 2023
- Lai Mohammed a baya-bayan nan ya yi martani, inda ya shawarci jam’iyyun biyu da su daina kuka su rungumi kaddara kawai game da zaben
- A martanin PDP, duk wani batu na APC ba komai bane face kokarin kawo tsaiko da kuma matsala ga karar da ta shigar a kotun zabe
Jam’iyyar PDP ta kara jaddada cewa, dan takararta na shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ne a zahirance ya lashe zaben 2023 da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu, Tribune Online ta ruwaito.
A cewar wata sanarwar da sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahad 30 ga watan Afrilu, ya caccaki ministan yada labaran Najeriya, Lai Mohammed game da bayanansa na baya.
Idan baku manta ba, Lai Mohammed ya shawarci ‘yan adawa da ke kalubalantar sakamakon zaben 2023 da su su rungumi kaddara kawai.
Buhari ma na goyon bayan tauye hakkin PDP, inji jigon jam’iyyar
PDP ta ce, shugaba Buhari ya yi irin wannan tsokaci na Lai Mohammed, inda kuma ta zargi ministan da yada kalaman yaudara kuma na karya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta kuma bayyana cewa, martanin ministan ba komai bane face tunzurawa irinta APC don ganin an zalunci jam’iyyun adawa a kotun zabe, rahoton TheCable.
PDP ta kuma kara da cewa, dukkan ‘yan Najeriya suna sane cewa Atiku ne ya lashe zabe, ba wai dan takarar apc Tinubu ba, musamman idan aka yi la’akari da sakamakon da aka tattara daga rumfunan zabe.
Gwamnatin APC ta saba shirga karya da yaudara
Da take sukar gwamnatin Buhari, PDP ta ce gwamnatin APC “ta yi kaurin suna wajen shirga karya da yaudara.”
Ana yawan musayar kalamai tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da jam’iyyun adawa game da sakamakon zaben shugaban kasar da ya samar da Tinubu na jam’iyyar APC.
A baya, Atiku Abubakar ya yiwa Tinubu wankin babban bargo, inda ya zargi Tinubu da kasancewa dan asalin kasar Guinea amma aka bari ya kama hanyar siyasar Najeriya ba tare da dogon binciken da ya dace ba.
Asali: Legit.ng