Gwamnatin Buhari Ta Tura Jirgin Sojin Sama Don Kwaso ’Yan Kasar da Suka Makale a Sudan
- Gwamnatin Najeriya ta tura jirgn da za su dauko ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan da ke fama da rikici a halin yanzu
- An ruwaito cewa, jirgon soji ne zai yi wannan aikin, kuma zai tafi da kayan abinci, ruwa da magunguna domin ba wadanda suka makale
- Kasar Sudan na fama da kazamin yakin cikin gida, lamarin da ke kara daukar hankali a duniya baya ga yakin Ukraine da ake yi yanzu
FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta tura a dauko mata ‘yan Najeriyan da suka makale a kasar Sudan yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke nahiyar Afrika.
A halin da ake ciki, gwamnatin ta tura jirgin sojin saman Najeriya ne domin yin wannan aikin mai muhimmanci na tabbatar da kwaso ‘yan kasar lafiya.
A tun farko, rahotanni a kafafen yada labarai sun bayyana yadda ‘yan Najeriya suka makale a Sudan yayin da yaki ke ci gaba da gudana a kasar.
Yadda jirgin zai yi hidimar kwaso daliban
A cewar wani sakon Twitter da hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ya wallafa, jirgin zai tafi da abinci, magani da kuma ruwa mai yawa domin tabbatar da kwasho ‘yan kasar cikin koshin lafiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakazalika, an ce ba kai tsaye za a dauko su daga Sudan ba, za a dauko su ne bayan da suka isa kasar Masar mai makwabtaka da Sudan.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar wacce Legit Hausa ta gani a shafin Twitter:
“Jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya samfurin C-130 na shirin tashi zuwa kasar Masar domin kwaso ’yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan.
“Jirgin zai je da tarin abinci, ruwan sha da magunguna da dai sauransu.”
Kasar Saudiyya ta kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan
A wani labarin, kunji yadda jirgin ruwan kasar Saudiyya ya yi jigilar dauko ‘yan Najeriya da ke zaune a kasar Sudan da ke fama da yaki a halin da ake ciki.
Rahoton da muke samo ya bayyana cewa, an dauko ‘yan Najeriyan ne tare da wasu mutane ‘yan asalin kasar Saudiyya.
Har yanzu, ana ci gaba da rikici a kasar Sudan, lamarin da ke kokarin daidaita kasar da mazauna cikinta a wannan karon.
Asali: Legit.ng