Shekau, Anini, Oyenusi Da Wasu Yan Ta'adda 2 Da Suka Addabi Najeriya

Shekau, Anini, Oyenusi Da Wasu Yan Ta'adda 2 Da Suka Addabi Najeriya

Matsalin rashin tsaro a halin yanzu a Najeriya ba sabon abu bane domin ko a shekarun baya an dade ana fama da shi sai dai salo ke canjawa.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wasu da dama ka iya cewa abin ya munana a yanzu kuma magance shi ya fi wahala. Duk da haka, a tarihi akwai wasu kallubalen tsaro da kasar ta yi fama da su cikin shekaru 30 da suka shude.

Hatsabibai
Wadannan mutanen sun aikata manyan laifuka kama daga fashi da makami, garkuwa da mutane da kisan kai da ta'addanci. Hoto: Photo: Daily Trust, Nigeria Voice NV
Asali: UGC

A cikin wannan gajeren rubutun, Legit.ng za ta yi nazari kan manyan hatsabiban bata gari da suka addabi Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

1. Lawrence Anini

Tabbas! Lawrence Anini, wanda aka fi sani da 'The Law' shine bata gari mafi muni a Najeriya a zamaninsa.

Ya yi kaurin suna wurin fashi da makami a shekarun 80s kuma ya halaka mutane da dama a tsohuwar jihar Bendel, wacce a yanzu ta rabu zuwa jihohin Edo da Delta.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Maganar Farko Da Ya Shiga Hannun Hukumar EFCC

Anini da tawagarsa sun aikata fashin banki da dama da hare-hare kan yan siyasa fitattu da masu hannu da shuni a yankin.

Yan sanda sun kama Anini a ranar 3 ga watan Disambar 1986 aka kai shi kotu. Mai shari'a James Omo-Agege ba babban kotun Benin, mahaifin Sanata Ovie Omo-Agege ne ya yanke masa hukuncin kisa.

An zartar masa da hukuncin tare da yan tawagarsa a 1987.

2. Ishola Oyenusi

Da dama za su iya cewa Ishola Oyenusi ya kamata ya zo na farko a jerin shahararrun yan fashi a Najeriya. Hakan gaskiya ne amma Anini ya kasance matsala ga kowa, ya fi kowa shahara.

Amma, Oyenusi da aka yi wa lakabi da 'The Doctor' shima dan ta'adda ne a zamaninsa, amma bai dade yana tafka ta'adi ba, ya yi hare-harensa a 1970 zuwa 1971.

An kama Oyenusi tare da yanke masa hukuncin kisa a 1971 kuma masana'antar fina-finai ta Nollywood ta shirya fim dangane da rayuwarsa. Za a iya tunawa da shi a matsayin dan fashin da ya yi murmushi har mutuwarsa, kalmar da jaridar da ta wallafa labarin kisarsa tare da hotonsa ta kirkira.

Kara karanta wannan

IMF Tayi Alkawarin Taimakon Najeriya Ganin Gyare-Gyaren da Bola Tinubu Ya Kinkimo

3. Baddo

Baddo ya jagoranci wata hatsabibin kungiyar asiri a Ikorodu, Jihar Legas. Kungiyar ta kashe mutane da dama tare da aikata munanan laifuka, amma daga karshe yan sanda sun kama Baddo sun kashe shi.

Wasu rahotanni sun ce a watan Yunin 2016, lokacin da yan sanda suka sako shi bayan tsare shi na kankanin lokaci, mazauna Ikorodu ne suka yi jarumta suka halaka Baddo suka cinna masa wuta.

4. Shina Rambo

Oluwasina Oluwagbemiga wanda aka fi sani da Shina Rambo, gawurtaccen bata gari ne kuma mai garkuwa da mutane a shekarun 90s.

Ya jagoranci manyan fashi da makami da hare-hare, ciki har da sace fitattun mutane, masu hannu da shuni da yan siyasa don karbar kudin fansa.

Daga bisani, an kama Rambo an tura shi gidan yari idan ya tuba ya zama kirista na gari.

Wani rahoton ya ce yana hanyarsa na zuwa Lanrewaju Motors don ya siya Pathfinder SUV a lokacin da yan sanda suka kama shi a Ojota New Garage.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An yi ram da wasu mazauna Qatar, rikakkun 'yan safarar kwaya a wata jiha

Daga bisani an rahoto cewa lokacin kokarin kama shi, ya yi kokarin kwace bindigan yan sanda amma wani dan sandan ya bindige shi nan take.

Amma, wani Mathew Oluwanifemi, tubabben mai laifi, wanda yanzu fasto ne, ya yi ikirarin shine Shina Rambo.

5. Abubakar Shekau na Boko Haram

Boko Haram babban matsala ce a Najeriya wacce ta yi fice tun shekarun 2000. Har yanzu akwai yan kungiyar a sassan Najeriya, inda suka kai hare-haren bama-bamai, sace mutane da wasu laifukan.

Sun kuma yi kaurin suna wurin kai wa jami'an gwamnati hari da jami'an tsaro.

A 2014, a wani hari mai muni da shugabansu Abubakar Shekau ya jagoranta a Chibok, wani kauye a Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, sun sace yan mata dalibai fiye da 2000.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Shekau ya kashe kansa ta hanyar tayar da rigar bam da ya ke sanye da ita sakamakon yaki da suke yi da shugaban tsagin kungiyar ta'addancin da ke biyayya ga ISIS. Abokin fafatawar Shekau, Abu Musab al-Barnawi, shima ya tabbatar Shekau ya kashe kansa.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Malamin Addinin Musulunci

Hare-haren Boko Haram ya yi sanadin miliyoyin mutane sun rasa muhallinsu tare da kashe dubban mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164