"Danginmu Na Da Kudi": An Kama Mata Da Miji Kan Garkuwa Da Kansu Da Neman Saboda Uwansu Su Biya N5m Don Fansa

"Danginmu Na Da Kudi": An Kama Mata Da Miji Kan Garkuwa Da Kansu Da Neman Saboda Uwansu Su Biya N5m Don Fansa

  • Wani magidanci dan shekara 53 da matarsa yar shekara 48 sun shiga hannun yan sanda a Legas kan zarginsu da garkuwa da kansu
  • Magidancin da aka kama ya amsa wa yan sanda cewa tabbas ya yi karyar garkuwa da kansa amma saboda yana son yan uwansa da ke turai su turo masa kudi ne
  • Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun yan sandan Legas ya tabbatar da afkuwar, yana mai cewa wanda aka kama ya ce gidansa ya ke son ya siya kan kudi N3m

Jihar Legas - Rundunar yan sandan Najeriya ta reshen jihar Legas ta kama wasu mata da miji kan zarginsu da garkuwa da kansu tare da neman fansar Naira miliyan 5, rahoton The Punch.

Mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, hakan a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

"Yana Iya Zautar Da Mutum": Yadda Matar Aure Ta Ci Amanar Mijinta Na Sunnah, Sam Ba Ta Yi Da Na Sani Ba

Ben Hundeyin
An kama ma'aurata da suka yi garkuwa da kansu a Legas don neman fansar N5m daga yan uwansu. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Hundeyin ya ce mijin, dan shekara 53 mai aikin hannu da matarsa, yar shekara 48 mai gyaran karaya, an kama su ne a ranar Laraba da Alhamis bayan wani dan uwansu ya kai korafin sace su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce mata da mijin, sun amsa laifinsu, sun yi ikirarin sun yi garkuwa da kansu ne da nufin samun Naira miliyan 3 don siyan gidansu da Badagry, Legas.

Kakakin yan sandan ya ce:

"Mutumin ne ya kawo shawarar matar ta amince. Bai musanta ba a gaban yan sanda. Ya ce ya aikata hakan ta sakon text ne saboda dalili. Ya ce ya yi hakan ne domin yana son ya sake siyan gidansa da Naira miliyan 3.
"Mutumin ya ce ya shirya garkuwa da kansa ne saboda yana da yan uwa masu hannu da shuni a kasar waje.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Mahaukaci Yake Tafiyan Kilomita Da Yawa Zuwa UNIBEN a Kullun, Ya Zauna Yana Rubutu

"Ya ce idan sun ji labarin sace shi da matarsa, za su sasanta da masu garkuwar kuma za su biya kudin."

Hundeyin ya ce mata da mijin suna zaune a gidansu da ke Badagry lokacin da suka tura wa yan uwansa sakon sace su, yana mai cewa lokacin da yan sanda suka ziyarci gidan a ranar Talata sun tarar da su tare da yayansu uku.

An kama matar a ranar Laraba yayin da shi kuma mijin aka kama shi a ranar Alhamis kamar yadda The Cable ta rahoto.

Ya kara da cewa za a gurfanar da su a kotu idan an kammala bincike.

An ceto wadanda aka yi garkuwa da su a tashar jirgi a Edo

A wani rahoton kun ji cewa bayan shafe kusan kwana bakwai an a hannun yan bindiga, gwamnatin jihar Edo ta ce ta ceto mutane goma sha biyu.

A cewar gwamnatin an yi nasarar ceto fasinjojin ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin DSS, Sojoji, yan sanda da kuma yan kato da gora da suka yi aikin ceton.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kame matashin da ya kwace waya, ya bi mata da gudu zai soka mata wuka a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164