Tinubu Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Dan Takarar Gwamnan Kogi Na APC, Ya Fadi Dalili

Tinubu Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Dan Takarar Gwamnan Kogi Na APC, Ya Fadi Dalili

  • Zababben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya karbi bakuncin dan takarar gwamnan jihar Kogi na APC
  • Tinubu ya bayyana goyon bayansa ga Hon. Ododo Usman, inda ya nemi ‘yan jihar su tabbata sun zabe shi a zaben Nuwamba
  • Yahaya Bello ya bayyana kwarin gwiwar cewa, ya zabo magajin da zai kai ga gaci a zaben da ke tafe nan ba da jimawa ba

FCT, Abuja - Awanni kasa da 48 bayan da Yahaya Bello ya nuna shi ga Buhari, Hon. Ododo Usman, dan takarar gwamnan APC a jihar Kogi ya kara samun karbuwa a idon manyan APC.

A yau Asabar 29 Afirilu, 2023 ne zababben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana goyon bayansa ga Ododo, rahoton Tribune Online.

Tinubu, wanda ya karbi bakucin Ododo a gidansa da ke Abuja ya bukaci mambobin APC a jihar Kogi da su yi aiki don ganin nasarar dan takararsu a zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kogi: Shugaba Buhari Ya Yarda Ododo Ya Gaji Yahaya Bello

Tinubu na goyon bayan Ododo
Ododo, Tinubu da Yahaya | Hoto: tribuneonlingng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, jihar Kogi ta kasance karkashin jam’iyyar APC tun 2015, kuma wannan babban nasara ne, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa, Ododo zai yi nasara a zaben watan Nuwamba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zababben shugaban ya kuma yabaawa shugabancin jam’iyyar APC da magoya bayan jam’iyyar bisa samun nasara a zaben da ya kammala.

Ododo ya cancanci ya gaje ni, inji Yahaya Bello

A tun farko, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya dauki Ododo zuwa ziyara, inda yace ya zabi Ododo ne a matsayin magajinsa saboda aminta, ganin zai iya kai ga nasara, jajircewa da kuma gogewarsa, The Whistler ta tattaro.

Yahaya Bello ya shaidawa Tinubu cewa, ‘yan Kogi za su zabi Ododo, saboda a ci gaba da yi musu ayyukan nasara da ci gaba da yake yi na tsawon shekaru bakwai na mulkinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa Tinubu, Hotuna Sun Bayyana

A watan Nuwamban 2023 da ke tafe ne za a yi zaben gwamnan jihar Gombe, wanda ya bambanta da sauran zabukan jihohi a Najeriya.

Tinubu ya shiga gidan gwamnati na Defence House

A wani labarin, kunji yadda Bola Ahmad Tinubu ya yi nasarar shiga gidan gwamnati na Defence House a makon jiya.

Wannan na zuwa ne bayan da ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya, kuma a gidan zai zauna har zuwa lokacin da za a rantsar dashi.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, Tinubu zai zauna tare da mataimakinsa., Kashim Shettima ne a gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.