“An Bar Wa Tinubu Jangwan”: Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Dage Kidayar 2023, Ya Gamo Shirin Buhari

“An Bar Wa Tinubu Jangwan”: Shehu Sani Ya Fadi Dalilin Dage Kidayar 2023, Ya Gamo Shirin Buhari

  • A kwanakin baya, gwamnatin jihar Benue ya nemi a dakatar da kidaya na 2023 da gwamnatin tarayya ke son yi a watan Mayun bana
  • Kwatsam, aka ji gwamnatin Buhari ya bayyana dage lokacin yin wannan kidaya zuwa wani lokacin na daban, ta bayyana dalili
  • Da yake martani ga wannan yunkuri na gwamnatin Najeriya, tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya ce gwamnatin ba ta da $1.8bn na yin kidayar, don haka ta kakabawa Tinubu aikin

Tsohon sanata daga jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta dage lokacin yin kidayar ‘yan kasa na 2023.

Sani ya bayyana dalilinsa a Twitter, inda yae gwamnatin Buhari ta dage aikin ne don bar wa Tinubu jangwan na kashe $1.8bn na kidayar a nan gaba.

Idan baku manta ba, Bola Ahmad Tinubu zai karbi ragamar Najeriya ne a ranar 29 ga watan Mayun da za mu shiga jibi.

Kara karanta wannan

1 Ga Watan Mayu: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Litinin a Matsayin Hutu Don Bikin Ranar Ma’aikata

Shehu Sani ya gano shirin Buhari na dage kidaya
Gaskiyar dalili ya fito daga bakin Shehu Sani | Hoto:Shehu Sani, Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari zai bar wa Tinubu aiki jangwan

A cewar Shehu sani cikin rubutunsa na Twitter Legit Hausa ta gani a ranar Asabar 29 Afirilu, 2023, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gaskiya mai sauki shine gwamnatin tarayya bata da $1.8bn na yin aikin kidaya sannan yanzu ta tura matsala ga Asiwaju.”

A bangare guda, ‘yan Najeriya sun yi ca game da batun Shehu Sani, inda suke bayyana ra’ayoyinsu game da Tinubu da kuma aikin kidayar gaba daya.

Wasu suna da ra’ayin cewa, Tinubu na da nagartar da zai iya yin wannan aikin ba tare da wata matsala ba, tare da cewa shi jajirtacce ne da ya kware wajen warware matsaloli.

Sai dai, wasu kuma suna kan ra’ayin cewa, akwai kamshin gaskiya game da batun na sanata Sani, inda suka ce gwamnatin Buhari dama ta kware wajen dauko abin da ba zai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: Zababɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, Ya Gana da Wasu Gwamnoni da Sarkin Kano

Shehu Sani ya saba dauko maudu’i game da halin da Najeriya ke ciki tare da bayyana matsayarsa da ra’ayinsa a kai.

Buhari ya dage kidayar ‘yan Najeriya na 2023

A rahotonmu na baya, kunji yadda gwamnatin Najeriya ta bayyana dage aikin kidayar jama’a da za a yi a watan Mayun bana.

Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar dage aikin zuwa wani lokaci nan gaba.

Wannan na nuna cewa, shugaban kasar ya bar wa gwamnatin Tinubu aikin kidayar da za a yi a cikin wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.