Yan Bindiga Sun Kai Harin Ɗakin Taron Jama'a, Sun Kashe Shugaban Al'umma

Yan Bindiga Sun Kai Harin Ɗakin Taron Jama'a, Sun Kashe Shugaban Al'umma

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun shiga ɗakin taro, sun kashe shugaban al'umma a jihar Imo da ke kudu maso gabas
  • Wata majiya ta bayyana cewa mamacin na cikin jawabi ga mahalarta taron, ba zato maharan suka shigo suka bindige shi
  • A makon da ya gabata wasu 'yan bindiga suka yi ajalin 'yan sanda biyar da kuma wasu ma'aurata a jihar Imo

Imo - 'Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Ngali, yankin Logara a ƙaramar hukumar Ngor Okpala, jihar Imo, inda suka harbe wani shugaban al'umma har lahira.

Leadership ta tattaro cewa shugaban mai suna, Chief Monday Eke, na cikin jawabi ga mutanen ƙauyen a ɗakin taro, ba zato yan bindigan suka kutsa kai.

Mahara.
Yan Bindiga Sun Kai Harin Ɗakin Taron Jama'a, Sun Kashe Shugaban Al'umma Hoto: leadership
Asali: Twitter

Maharan, waɗanda suka zo a cikin jar Mota Camry, suna zuwa suka harbe mutumim har lahira kana daga bisani suka koma inda suka fito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida, Sun Yi Garkuwa da Sarki Mai Martaba a Arewacin Najeriya

Wata majiya a yankin, wanda ya nemi a sakaya bayanasa ya ce mamacin Chief Monday, ya kasance direban da ke aiki da Motar Tifa mallakin wani mutumi a garin Umuohiagu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa ita kanta motar da maharan suka zo a cikinta fashinta suka yi daga hannun Mista Obum, wanda ya kawo ziyara garin domim ɓinne mahaifiyarsa, kuma 'yan bindigan sun aje motar a wani wuri.

A rahoton Sunnews, Mutumin ya ce:

"Yan bindigan sun zo a shirye ɗauke da manyan makamai kuma sun rufe fuskokinsu. Hakan ne ya sa kowa ya shiga damuwar kan ko akwai Imfoma."
"Haka a watan da ya shuɗe, mutumin da duk mun san shi, Papa Mayor, yan bindiga suka je har gida suka kashe shi. Bamu san me ke shirin faruwa a garin mu ba."

Idan baku manta a makon da ya gabata, aka halaka yan sanda biyar da wasu ma'aurata a mahaɗar titunan Okpala, jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Yan Farin Hula 15 Da Sojoji 2

An sace basarake mai martaba a Zamfara

A wani labarin kuma Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hakimi a Jihar Zamfara

Yan fashin daji da suka addabi mutane a jihar Zamfara sun yi awon gaba da hakimin kauyen Kasuwar Daji, ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda.

Mazauna garin sun bayyana cewa maharan ba su taɓa kowa ba, kai tsaye suka wuce gidan basataken, suka tafi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262