“ChatGPT Ya Cuce Ni”: Yadda Wata Budurwa Ta Samu Makin 0 a Jarrabawa Bayan Amfani da GPT
- Wata daliba ‘yar Najeriya ta bayyana yadda lakcaranta ya bata makin sufuri saboda satar amsa a jarrabawar da ta yi
- A takardar jarrabawar da ala yada, lakcaran ya ce tabbas ta yi amfani da na’ura mai kwakwalwa ne wajen rubuta jarrabawar
- Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mamaki, inda suka yi martanin Allah-wadai da kwafin bayanai daga na’ura a jarrabawa
Wata ‘yar Najeriya ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ta yada bidiyon takardar amsar jarrabawar da ta yi.
Budurwar ta ce an ba ta takardar jarrabawar, inda ta ga an ba ta makin sufuri, lamarin da ya ba ta mamaki har ta yada batun.
Lakcaran da ya yi makin takardar jarrabawar ya bayyana karara cewa, ya ba ta sufuri ne saboda ta yi amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen tattara bayanai.
“Auren Nan Ba Zai Yiwu Ba”: Uba Ya Ba Kowa Mamaki a Wajen Bikin Diyarsa, Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Bidiyo
Da take yada bidiyon, budurwar ta ce manhajar ‘komai na sani’ na ChatGPT ya karar da ita. Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mata martani mai zafi, inda suka ce budurwa bata iya komai ba, kawai kwafe komai tayi ba tare da gyarawa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kafar Instablog9ja ce ta yada bidiyon a manhajar Instagram, kalli bidiyon a nan:
Martanin jama’ar kafar sada zumunta
Artfarihub:
“Abin da ya kamata ta kwafe ta kai Quillbot don sauya shi..daga nan kuma watakila ga paraphraser.io AI ya maida shi kamar mutum daga karshe.”
Chinonso_:
“Lol. Idan kika yi amfani da ChatGPT wajen rubutu, ya kamata ki mayar dashi kamar rubutun mutum ya zama naki. Daidai yake da kwafin aikin wani da lambarsa a dakin jarrabawa, lakcara zai gane satar amsa kika yi.
“Akwai wani shafin intanet inda bayan rubutu, za ki iya duba rubutun ko ya yi kama da rubutu ChatGPT.
_deagram:
“ChatGPT na kai wa ga rashin zurgin tunani. Bai kamata ya zama shine tushen samun bayanai ba, musamman ga dalibai.”
Nkonyeasoa:
“ChatGPT abu ne mai kyau, amma sai ga mutane masu wayo ne za su gane yaya ake aiki dashi. Abu mafi sauki ne ki tambayi chat GPT ya ba ki bayanin da bai yi kama da na na’ura ba zai sa ki samu maki daga 0 zuwa 100.”
Fheytii:
“Ta yaya lakcaran ya gano hakan? Omo.”
Thelope__':
“Mutane basu gane hanyar wannan abin ba. Idan za ka yi amfani da AI, ki bibiyi amsoshin da ya bayar sannan ki kara wasu bayanai masu kama da na mutum, ki ba shi haske da tsari mai kyau. Idan zai yiwu, ki ma sake rubuta komai.”
Fasaha na ci gaba da kara yawa, an yi wani otal inda mutum-mutumi ke kawo abinci a madadin mutum.
Asali: Legit.ng