Matashi Ya Gamu da Fushin Alkali Bayan Watsawa Budurwar da Abokin Nemansa ‘Acid’
- An yankewa wani matashi hukuncin shekaru bakwai a gidan yari bisa zarginsa da aikata laifin cutar da budurwarsa da abokin nemansa
- An gano cewa, ya watsa musu ruwan ‘acid’ mai kone fata a lokacin da suke kwance a dakin otal, lamarin da ya jawo tashin hankali
- A rahoton da muka samo, an bayyana dalla-dalla yadda ya aikata laifin da kuma hukuntashi da aka yi daidai laifinsa a kotu
Jihar Legas - Mai shari’a Oyindamola Ogala ta babbar kotun jihar Legas a ranar Laraba ta yankewa wani kafinta mai shekaru 32, Onyekachi Agu hukuncin shekaru bakwai bisa laifin wanke tsohuwar budurwarsa Aishat Adefarati da abokin nemansa, Mansur Ahmad ruwan ‘acid’ a 2020.
Mai shari’a Ogala ta tura matashin magarkama ne shari’ar da aka yi ta kama matashin da laifin cutar da jikin dan Adam, karar da gwamnatin Legas ta shigar, Leadership ta ruwaito.
Jami’ar ‘yar sanda mai gabatar da kara, Uju Uwangaze ta sanar da mai shari’a cewa, wanda aka gurfanar din ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Yunin 2020 a otal din Gangare da ke Mile 12 a Legas.
A ina ya same su ya watsa musu ruwan ‘acid’?
Uwangaze ya kuma bayyana cewa, wanda aka gurfanar din ya bibiyi saurayi da budurwar ne a otal din tare da watsa musu ‘acid’, laidin da ya saba da sashe 245 na kudin manyan laifukan jihar Legas, 2015.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A lokacin da ake titsiye shi, Agu ya ce, ya taba dirkawa budurwar tasa ciki, amma kuma ta zubar dashi, lamarin da bai masa dadi ba, rahoton The Guardian.
A bangarenta, tsohuwar budurwar tasa ta ce, Agu yana da dabi’ar hantararta, wanda ya jawo suka gimtse alakarsu ta shekaru uku.
An kama Agu da laifin cutarwa, ya amsa da kansa
Mai shari’a Ogala ta kama Agu da laifin cutar da mutum biyu, inda da kansa ya amsa cewa ya aikata laifin, wannan yasa ta yanke masa hukuncin da ya dace dashi.
Mai shari’a ta ce, amsa laifinsa da ya yi da kuma hujjojin da aka gabatar a gaban kotu ne suka sa aka yanke masa hukunci.
Kotun ta kuma bayyana cewa, wanda aka gurfanar din ya zo wasa da hankalin kotu, wanda a baya ya amsa aikata laifin amma daga baya yace bai yi ba.
Irin raunukan da aka samu
Mai shari’a ta ce, abokin neman nasa, Mansur Ahmed ya samu mummunan kuna a fuskarsa, idonsa, wuyansa da ma kudaden da ke cikin aljihunsa.
Hakazalika, ta bayyana cewa, raunin da ke jikin wanda aka gurfanar din ya same shi ne a lokacin da ya aikata barnar a cikin otal din.
A wani labarin, kunji yadda wani mutum ya bakawa gidan su budurwarsa wuta bayan da suka samu sabani ta soyayya.
Asali: Legit.ng