Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Miliyan 560 Wajen Ceto ‘Yan Najeriya a Kasar Sudan

  • Motoci kimanin 40 za su dauko ‘Yan Najeriya da yakin da sojoji suke yi ya rutsa da su a Sudan
  • Za a bi ta titi har a shiga kasar Masar, daga nan sai an yi amfani da jiragen sama domin a zo Najeriya
  • Gwamnatin tarayya ta ce wannan zirga-zirga na ‘yan kwanaki za ta ci abin da ya kai Dala miliyan 1.2

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce abin da ta kashe domin dauko wasu ‘Yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan da ake yaki, ya kai Dala miliyan 1.2.

Vanguard ta ce wadannan makudan kudi sun kai kimanin Naira miliyan 560. Wani abin farin cikin kuma shi ne babu ‘Dan Najeriya da aka kashe a yakin.

Gwamnatin Najeriya ta tattara mutanenta daga kasar Arewa maso gabashin Afrikar, za a bi ta titi har zuwa kasar makwabta, daga nan ne sai a shiga jirgi.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

Karamin Ministan harkokin kasar waje, Ambasada Zubairu Dada ya yi wannan bayani da yake zantawa da manema labarai bayan taron FEC a Abuja.

"Babu wanda zai mutu" - Najeriya

Ambasada Zubairu Dada ya shaidawa ‘yan jarida su na sa ran babu ko rai daya da za a rasa a Sudan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dada ya ce a lokacin (ranar Laraba), Darekta Janar na hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa yana bakin iyakar Masar domin karbar ‘Yan Najeriyan.

Jirgi
Wani jirgin sama a samaniya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Saboda ganin an ceto ‘Yan kasar, Ministan yake cewa jami’an hukumar da ke kula da masu ci-rani a ketare sun tare a kasashen Masar da Habasha.

Ma’aikatan ne za a damkawa wadannan mutanen Najeriya da suka biyo ta motoci 40 daga Khartoum, sai dan dauko su sannan za a dauko jakadu.

Kokarin Gwamnatin Saudi

A wani rahoto na Daily Trust an fahimci cewa tuni gwamnatin kasar Saudi Arabiya ta dauke wasu ‘Yan Najeriya ta teku, abin da ya jawo yabon Ministan.

Kara karanta wannan

Motocin Da Za Su Kwashe Yan Najeriya a Sudan Sun Isa Garesu a Bidiyo

Ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama ya ce an fuskanci wasu kalubale wajen ganin an dawo da mutanen Najeriyan daga inda yaki ya barke.

Geoffrey Onyeama yana sa ran ba da dadewa ba komai zai zama tarihi, a cewarsa da zarar motocin da aka dauko sun isa, za a dawo da kowa ta jirgin sama.

Yaki ya kaure tsakanin sojoji

A baya kun samu rahoto ana cikin zaman tashin hankali, Gwamnatin tarayya ta na neman hanyar da za a iya kubuto da ‘Yan Najeriya ta hanyoyin mota.

Lamarin ya faskara wajen shiga kasar Ethiopia, amma an yi sa’ar shawo kan mayakan, gwamnatin kasar Amurka za a tsagaita wuta na awa 72.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng