Saura Kiris a Rantsar Dasu, Tinubu da Shettima Sun Koma Gidan Gwamnati Na Defence House
- Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bai dauki batun rantsar dashi da wasa ba yayin da ranar 29 ga watan Mayu ke kara gabatowa
- Dalili kuwa, tuni Tinubu ya tattara ya koma Defence House, wani gidan gwamnatin Najeriya gabanin rnatsar dashi, kamar yadda bidiyo ya nuna
- A bangare guda, Buhari ya ce ya gaji da tukin motar Najeriya, ya matsu ya ba Tinubu ya ci gaba daga inda ya tsaya
FCT, Abuja – Zabebben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya yi kaura daga gidansa zuwa Defence House, gida mallakin gwamnatin Najeriya gabanin rantsar dashi a watan gobe.
Ana tsammanin dama Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima za su koma Defence House, inda za su zaina kafin daga bisani su koma Villa bayan karbar mulki, rahoton The Guardian.
Wannan na nufin, daga lokacin da Tinubu ya lashe zabe, yana da damar fara amfani da kayayyakin gwamnatin tarayya.
A bidiyon da aka yada a Twitter na lokacin da Tinubu ke kaura tare da mataimakinsa, ‘yan Najeriya da yawa sun shiga matukar mamaki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meye yasa Tinubu zai koma Defence House?
Defence House dai wani gida ne da gwamnatin Najeriya ta gina musamman don zababben shugaban kasa ya shiga kafin karbar mulki, an fara hakan ne a 1999.
Daraktan yada labaran Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya tabbatar daukarar Tinubu zuwa gidan a ranar 26 ga watan Mayu a shafinsa na twitter.
A cewarsa, zababben mataimakin shugaban kasa da zababben shugaban kasa za su zauna a gidan nan da ranar 29 ga watan Mayu.
A kalamansa:
“Zababben shugaban kasa Bola Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima sun kaura zuwa gidan gwamnati gabanin rantsar dasu a ranar 29 ga watan Mayu.”
Na matsu na mika mulki ga Tinubu
A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, ya kagu ya maida mulkin nan hannun zababben shugaban kasa Bola Tinubu.
Shugaban ya ce, zai koma jiharsa ta Katsina, musamman garinsu Daura don ci gaba da zama da ahalinsa a can.
Ba wannan ne karon farko da Buhari ke bayyana aniyarsa ta barin Abuja zuwa jiharsa ba, ya sha fadin hakan tun kafin ma a yi zaben shugaban kasa na bana.
Asali: Legit.ng