Tinubu Bai Cancanci Mulkin Najeriya Ba, Atiku Ya Ballo Wa Tinubu Ruwa Ana Dab da Rantsar Dashi

Tinubu Bai Cancanci Mulkin Najeriya Ba, Atiku Ya Ballo Wa Tinubu Ruwa Ana Dab da Rantsar Dashi

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP ya ci gaba da bayyana matsayarsa cewa, Tinubu na APC bai yi nasara ba a zaben bana
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a martaninsa ga bayanin Tinubu game da karar ya shigar a kotun zabe
  • Tinubu da APC sun yi watsi da daukaka karar Atiku, inda suka bayyana shi a matsayin dan takarar da ke fitowa duk sadda zabe ya taso

FCT, AbujaDan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce, ya kan fito takarar shugaban kasa tun 1993 ba tare da wata matsala ko tuhuma ba kamar yadda aka yiwa Bola Tinubu.

Bayanin Atiku wani martani ne ga yadda Tinubu da APC suka yi masa shagube game da yawan fitowa takara tare da rashin yin nasara a kowanne lokaci, kamar dai a 2023.

Kara karanta wannan

Faɗuwa Zaɓe: Atiku Ya Yi Wa Tinubu Gori A Martanin Da Ya Mayar Masa

A gefe guda, Atiku ya ce, komai nasa daram yake kuma na gaske, kama daga shaidar dan kasa, shekaru, jihar da aka haife shi da takardun karatu; ba kamar Tinubu ba.

Tinubu bai cancanta ba, inji Atiku Abubakar
Tinubu na jam'iyyar APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A martaninsa ga bayanin Tinubu, Atiku ya ce, a bisa tsarin dokar Najeriya, Tinubu bai cancanci zama shugaban kasa ba a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Najeriya na shakkar sahihancin Tinubu

Ba Atiku kadai ba, ‘yan Najeriya da yawa sun nuna damuwa da cewa, Tinubu bai cancanta ba saboda wasu dalilai da ke kasa.

A martanin Atiku ta hannun lauyansa, Chief Chri SAN, ya bayyana dalla-dalla dalilinsa na cewa Tinubu ba cikakken dan Najeriya bane.

A martanin da Legit.ng ta samo na Atiku, ya ce:

“Tinubu na da shaidar zama dan kasa kala biyu na Najeriya da na Guinea, wanda da kansa ya nemi shaidar zama dan kasar Guinea.

Kara karanta wannan

Ahaf: Sirri ya fito, an fadi gaskiyar alakar Tinubu da kasancewarsa dan kasar Guinea

Bugu da kari, Atiku ya zargi Tinubu da rashin bayyana gaskiyar bayanansa kamar yadda dokar INEC ta tada a cikin fom din da ‘yan takara ke cikawa na EC9.

Don haka yace, nasarar Tinubu a zaben 2023 ta saba doka, bata cancanta ba kuma ya saba da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Alakar Tinubu da kasar Guinea

Sai dai, a wani bayanin da ya fito daga bakin wani jigon Najeriya, ya bayyana gaskiyar alakar Tinubu da kasancewa dan kasar Guinea.

Yara ya bayyana cewa, Tinubu ya karbi shaidar zama dan kasar Guinea ne a matsayin karrama shi da kuma ba shi lambar yabo.

Ya ce, hakan bai nufin Tinubu cikakken dan kasa ne, wanda hakan zai hana shi mulkin kasar nan a nan gaba ko yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.