Sojoji Sun Sheke ’Yan Bindiga 5, Sun Kwato Alburusai, Shanu da Tumaki a Zamfara
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka wasu tsagerun ‘yan bindigan da suka addabi jama’a a yankunan jihar Zamfara
- Sun kuma kwato kayayyakin aikata laifi, ciki har da bindigogi da sauran muggan makamai da ake aikata barna dasu a Arewa
- Hakazalika, an kwato wasu mutanen da ‘yan bindigan suka sace da nufin tafiya dasu domin neman fansa daga ahalinsu
Bakura, jihar Zamfara - Dakarun Operation Hadarin Daji sun sheke akalla ‘yan ta’adda biyar a wata bata-kashi da suka yi da ‘yan ta’addan a wani yankin jihar Zamfara.
Channels Tv ta ruwaito cewa, dakarun sun yi wannan aikin ne a lokacin da suke aikin sintiri a yankin Damri da karamar hukumar Bakura ta jihar.
Kafar ta kuma bayyana cewa, sojojin sun samu bayanan sirri na gaskiya game da motsin ‘yan bindigan da tulin shanun da suka sato.
Yadda sojoji suka kai dauki
A cewar rahoto, nan take sojojin suka gaggauta damara tare da taran ‘yan bindigan a kauyen Galadimai da ke lardin Damri a karamar hukumar ta Bakura.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan kicibus da suka yi, an sheke ‘yan bindiga uku nan take, inda wasu daga cikinsu kuwa suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan bindigan sun hada da AK47 gida daya da kuma alburusai masu girman 7.62mm, da kuma babura gida biyar. Bugu da kari, sun kwato shanu, rakuma da tumaki da yawa.
An sheke ‘yan bindiga biyu a wani yankin na daban
A wani yanayi irin wannan, dakarun sojojin da ke sintiri a yankin Magami sun amsa kiran gaggawa na yadda aka zo yin awon gaba da wasu mutum shida a yankin. An ce sojojin sun isa wurin da lamarin ya faru nan take.
Da suka hango sojoji, ‘yan ta’addan sun bude wuta a kansu tare da tsere da mutanen da suka sacen zuwa cikin daji.
Bisa kokarin soji, an yi nasarar ceto wasu da aka sacen, yayin da wasu kuma tsere don tsira da rayukansu, wanda a yanzu haka ana neman inda suka shiga don ceto su.
Aan hallaka ‘yan bindiga biyu a farmakin yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga. An kwato AK47 guda daya, harsasai da kuma bindigar harba bam, kudi N3,700 da kuma mujallun alburusai guda biyu.
A Benue, an kama wasu matasan da suka binne wani tsoho da ransa bisa zargin yana aikata maita a yankin.
Asali: Legit.ng