Da Yawan Manyan Gidajen Abuja da Legas an Samar Dasu Ne Daga Kudaden Rashawa, Inji EFCC

Da Yawan Manyan Gidajen Abuja da Legas an Samar Dasu Ne Daga Kudaden Rashawa, Inji EFCC

  • Hukumar EFCC ta yi bayanin cewa, alamu sun nuna gidaje da yawa a Abuja da Legas mallakin ‘yan rashawa ne
  • Wannan na fitowa ne daga bakin wasu manyan jiga-jigan hukumar, inda suka ba da shawarin yadda za a kula
  • A kasar nan, ana yawan samun lokutan da ‘yan rashawa ke barna tare da sace kudin al’umma don azurta kansu

Jihar Edo - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya (EFCC) ta ce tana aikin kakkabewa da tona sirrin barayin da ke basaja da gidaje da wasu kadarori a kasar.

Da yake bayani ga manema labari game da tasirin EFCC wajen yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Benin ta jihar Edo, lauyan hukumar, Chris Mishela ya ce, da yawan gidaje a Abuja, Legas da wasu sassan kasar na da alaka da kudin rashawa.

Kara karanta wannan

Na Sha Wahala Da Ita: Wani Ya Kashe Budurwarsa Saboda Tayi Watsi da Soyayyar Shi

EFCC ta sha kama kadarori da suka hada da gine-gine da sauran kayayyaki masu daraja a kasar da ke da alaka da rashawa da cin hanci, Daily Trust ta ruwaito.

EFCC ta gano sirrin barayi a Najeriya
Jami'an hukumar EFCC a bakin aiki | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Matakin da EFCC ke dauka kan ‘yan rashawa da masu satar kudin jama’a

A cewarsa, hukumar EFCC tana aiki tukuru don tabbatar da yaki da rashawa, kana za ta kawo sabbin hanyoyi a dokarta ta dakile sace-sacen kudin al’umma daga jami'an gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara bayani da cewa, hukumar na ci gaba da ankarar da ‘yan jarida game da sabon shiri da dokar yaki da rashawa na 2022 da kuma inda za su ba da gudunmawarsu.

Ya kara da cewa, sabuwar dokar ta yi kwaskwarima ne tare da fadada dokar yaki da rashawa ta 2011, rahoton Pulse.

Shawari kan yadda za a kula da damfara ta yanar gizo

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Inda Aka Kwana Kan Batun Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

Shugabar sashen yaki da damfara ta yanar gizo ta EFCC a Benin, Mrs Oluwakemi Olawoyin a bayaninta ta bayyanawa jama’a tasirin kiyayewa da kuma mai da hankali a hada-hada ta yanar gizo.

Ta ba da shawarin cewa, ‘yan Najeriya su guji latsa duk wani likau na yanar gizo da basu tabbatar da ingancinsa ba don gudun asara.

Hakazalika, ta yi tsokaci da ba da misalai na yadda za a kula da dukiya a lokutan musayar kudi ta intanet.

Ba wannan ne karon farko da ake ba ‘yan Najeriya shawarin yin taka tsan-tsan da ‘yan damfara ba game da dukiyoyin ‘yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.