An Ga Tashin Hankali Yan Bindiga Sun Budewa Yan Sanda 5 Wuta Yayin Da Suke Tsakar Cin Abinci A Ranar Idi A Imo
- Yan bindiga sun hallaka mutane 7 ciki har da jami'an yan sanda biyar tare da awon gaba da bindigun su
- Wani shaidar gani da ido ya ce yan bindigar sun bude wuta kan yan sandan yayin da suke cin abinci inda suka kashe uku nan take tare da bin biyu har maboya
- Rundunar yan sandan jihar Imo ta ce ba ta da masaniya akan lamarin amma za ta bincika tare da dawo da rahoto
Jihar Imo - Da safiyar Juma'a wasu yan bindiga sun hallaka yan sanda biyar a Okpala da ke karamar hukumar Ngor Okpala da ke Jihar Imo.
Sun kuma kashe wasu ma'aurata mata da mijinta Chinaka Nwagu da suka fito daga yankin Amankwo Okpala, rahoton The Punch.
Lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a gaba daya wanda hakan ya janyo tsayawar kasuwanci a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganau ya yi bayanin dalla-dalla yadda abin ya faru
Wani mai suna Uche wanda ya ce shi dan uwa ne ga ma'auratan da aka kashe ya shaidawa wakilin majiyarmu cewa jami'an yan sanda sun shigo daga ofishin yan sanda da ke Abo Mbaise don cin abinci a yankin.
Ya ce daidai lokacin da yan sandan ke cin abincin, wasu yan bindiga suka shigo wurin tare da bude musu wuta, Leadership ta rahoto.
Ya ce a take yan sanda uku suka mutu a wajen, yayin da biyu suka gudu zuwa wani shago da ke kusa amma maharan sun bi su shagon sun kashe tare da kashe ma'auratan da suka mallaki shagon.
Shaidar gani da idon ya ce bayan sun kashe yan sandan, yan bindigar sun kwashe bindigunsu sun gudu.
Shaidar ya ce:
"Wannan mummunar Juma'a ce ga yankin mu. Yan bindiga da misalin 8:00 na safe sun kashe yan sanda biyar a Okpala. Yan sandan sun zo da farar Hilux don cin abinci daga ofishin Aboh Mbaise don cin abinci.
"Soyayya Ta Gaskiya": Yadda Bidiyon Wasu Ma'aurata Yan Unguwar Mallam Shehu Ya Ja Hankalin Masu Kallo Miliyan 1
"Suna tsaka da cin abincin, yan bindiga sun shigo wajen sun bude musu wuta. Biyu daga ciki suka gudu wani shaho da ake siyar da ruwa da cincin (meat pie). Bayan kashe yan sanda uku, sun zo shagon da biyun suka boye, sun kashe su. Sun kuma kashe masu shagon mata da miji.
"Sun dauki bindigun su sun gudu. Wannan abin takaici ne. Ana zubar da jini a yankin mu. Kowa ya rude. Ma'auratan sun baro Lagos kimanin shekara guda. Yanzu muka kai gawarsu dakin adana gawa. An rufe kasuwa. Mutane sun gudu saboda tsoro da mamaki."
Wani sahidan gani da ido shima ya magantu
Wani shaidar, Dominic Okpor, ya shaidawa wakilin majiyarmu cewa ya ga gawarwakin jami'an lokacin da ya ke tuki a titin Owerri-Aba.
Okpor ya bayyana abin a matsayin abin takaici.
"Muna ganin gawarwakin yan sanda yashe a titi lokacin da muke tuki. An ajiye Hilux dinsu a gefe. Wajen ba kyan gani. Akwai bakin ciki. Allah ya sauwake."
Martanin yan sanda
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce bai samu labarin ba.
Ya dai dauki alkawarin zai dawo gare shi amma hakan bai samu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Wakilin majiyarmu ya yi tuni cewa ko a 27 ga Maris sai da yan bindiga suka kashe jami'an Civil Defence biyar a dai karamar hukumar ta Ngor Okpala.
Yan bindiga sun kona ofishin yan sanda, sun halaka jami'i guda a Imo
A wani rahoton, kun ji cewa wasu maharan sun afka ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Oguta a Jihar Imo sun cinna wuta.
Daily Trust ta rahoto cewa sun halaka jami'i guda yayin harin amma yan sanda da ke bakin aiki sun fatattake su.
Asali: Legit.ng