Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

  • Atiku Abubakar ya taya Musulmai murnar kammala azumin Ramadan da bikin karamar sallah
  • Wazirin Adamawa ya ce zaben da aka yi a 2023 ya taimaka wajen kara raba kan ‘Yan Najeriya
  • Kamar dai Alhaji Atiku Abubakar, Bola Tinubu ya fitar da jawabinsa na Barka da shan ruwa

Abuja - Atiku Abubakar ya ce halin da kasar nan ta shiga na rabuwar kai a sakamakon zaben shugaban Najeriya da aka yi, yana ci masa tuwa a kwarya.

A wani sakon barka da Sallah da Atiku Abubakar ya aikawa Musulman Najeriya, The Cable ta ce ‘dan siyasar ya koka a kan yadda sabani ya shiga al’umma.

‘Dan takaran shugaban kasar ya fitar da jawabi a ranar Alhamis bayan an sha ruwa, yake cewa abin da ake bukata shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Ka zo Ukraine: Shugaba Zelensky ya taya Tinubu murnar lashe zabe, ya yi masa gayyata ta musamman

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga Musulmai da su dage wajen ganin an samu hadin-kai a yanzu da siyasa ta jawo mummunan rabuwar kai.

Muhimmancin azumin Ramadan

Da yake magana, Atiku Abubakar ya yi wa Musulmai barka da buda baki bayan kammala azumi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, jama’a sun ga muhimmancin kauracewa miyagun laifuffuka, ya ce Ubangiji ya umarci Musulmai da hakan ne saboda amfanin karon kansu.

Atiku
Bala, Atiku, da Namadi a masallaci Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

"Kasa babu lafiya a yau" - Atiku

“Ka da mu yaudari kan mu. Kasarmu ta samu rabuwar kai sosai. Makomar zaben shugaban kasa ya sake jagwalgwala komai, wannan abin yana damu na.

- Atiku Abubakar

Kamar yadda Wazirin Adamawa ya nemi Musulmai su tuna kasar Najeriya a wajen addu’o’in idi, Bola Tinubu ya fitar da jawabinsa na taya su barka da sallah.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

A sakonsa na barka da shan ruwa, The Nation ta ce zababben shugaban kasar ya godewa Ubangiji SWT da ya bada damar ganin karshen azumi da zuwan idi.

Tinubu yake cewa baya ga kasancewar azumi daya daga cikin manyan ibada a addinin Musulunci, halin Bayin Allah ya canza da zuwan watan Ramadan.

Buda baki a Saudi

Rahoto ya zo a baya cewa Shugaban kungiyar Izala, Limaman babban masallacin Abuja da na Aso Rock sun sha ruwa tare da shugaban kasa a kasar Saudi.

An yi wa Najeriya da Gwamnati mai shirin karbar mulki addu'a yayin da wa’adin Muhammadu Buhari ya zo karshe, zai mika mulki a karshen watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng