Shagalin Sallah: Rundunar Yan Sanda Ta Kama Yan Daba a Jihar Bauchi
- Hukumar yan sanda ta kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka mutum 26 ana dab da sallah a jihar Bauchi
- Kakakin hukumar yan sanda, SP Ahmed Wakil, ya gargaɗi duk wani mai mugun nufi a lokacin shagalin Sallah ya shiga taitayinsa
- Idan har an ga watan Shawwal, gobe Jumu'a ɗaukacin Musulmai zasu gudanar da Idul Fitr, idan kuma ya ɓuya sai ranar Asabar
Bauchi - Rundunar 'yan sanda ta gargaɗi dukkan masu aikata muggan laifuka, da ke shirin kulla makircin ta da zaune tsaye lokacin ko bayan karamar Sallah su canja tunani ko su fuskanci fushin doka.
Vanguard ta tattaro cewa rundunar 'yan sandan ta kuma sanar da cafke 'yan daban siyasa 26 a sassan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Duk wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan, SP Ahmed Wakil, ya fitar ranar Talata a Bauchi.
Ya shawarci duk masu niyyar aikata muggan laifuka da ka iya kawo tasgaro ga zaman lafiya su tattara su bar jihar Bauchi domin babu wata ƙofar ɗa zasu aikata mummunan nufinsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
SP Wakil ya tabbatar da cewa nauyin da ke kan yan sanda na kare dukiya da kadarorin mazauna Bauchi, tabbatar da bin doka da oda da sauransu, na nan kuma sun shirya tsaf.
Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa hukumar zata ci gaba da zaƙulo duk wasu masu mugun nufi iyakar iyawarta kuma duk inda suka shiga zasu shiga hannu.
Yan sanda sun kama mutane 26
Ya ce rundunar dawo da zaman lafiya karƙashin jagorancin kwamanda, yayin wani Sintiri da suka fita sun kama 'yan daba 26 a wurare daban-daban a faɗin jihar.
A cewarsa, daga cikin abubuwan da suka kwato hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da Wuƙaƙe uku, Adduna guda 4, kanan wuƙaƙe masu kaifi da sauransu.
"Yayin bincike sun amsa laifukansu cewa suna cikin 'yan Sara Suka da ke aikata ta'addanci a tsakanin al'umma. Dukkansu zasu gurfana a gaban Kotu bayan gama bincike."
A wani labarin kuma Babbar Tashar Watsa Labarai a Najeriya Ta Kama Da Wuta a Watan Azumi
Wata tashar watsa labarai mallakin gwamnati ta kama da wuta sakamakon haɗuwar wayoyin lantarki.
Rahotanni sun nuna cewa wutar ta fara ne daga ɗakin watsa shirye-shirye kuma ana tsammanin ta tafka ɓarna mai yawa.
Asali: Legit.ng