Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

  • Majalisar wakilai ta na bincike kan zargin saida gangunan danyen mai miliyan 48 da aka yi a kasar Sin
  • Sakamakon binciken ya fara nuna cewa an batar da $200m ba tare da an bi dokar kasa da ka’idoji ba
  • A dalilin haka ake neman Abubakar Malami da Zainab Ahmed, amma duk sun ki zuwa gaban kwamiti

Abuja - Kwamitin majalisar wakilan tarayya da ke bincike a kan zargin saida gangunan danyen mai miliyan 48 a kasar Sin yana cigaba da aiki.

Rahoton The Cable ya ce wannan kwamitin bincike yana ikirarin gano wasu Dala miliyan 200 da aka biya a matsayin kudin aiki ba tare da ka’ida ba.

Binciken ya ce Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ya biya wadannan biliyoyi ne da sunan masu tonon silili.

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani

Shugaban kwamitin, Hon. Mark Gbillah ya bayyana haka yayin da ‘yan kwamitinsa suka cigaba da yin zama a majalisar wakilan tarayya a garin Abuja.

Malami da Ahmed za su yi bayani

Jaridar ta ce Mark Gbillah ya kuma koka a kan yadda Abubakar Malami da Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed suka ki ba kwamitin na sa hadin-kai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan majalisar yake cewa sun samu hujjojin daga ofishin Akanta Janar da ke nuna Ministar kudi ta amince a batar da $200m ba tare da an bi ka’ida ba.

FEC a Aso Rock
Ana taron FEC a Aso Rock Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

An kashe kudi ne da nufin a sallami masu fallasa laifuffuka, kwamitin ya ce ba a iya yin gamsashen bayanin inda kusan Naira Biliyan 92 suka shiga ba.

Ina kudin da ake ganowa su ke?

Baya ga haka, kwamitin ya ce su na ta jin labarin gwamnatin tarayya ta gano kudi ta karkashin tsarin tonon silili, amma har yau ba su ga kudin nan ba.

Kara karanta wannan

Bayan Kwashe Shekaru Ana Aiki, Daga Karshe Ministan Buhari Ya Bayyana Ranar Kammala Titin Kaduna-Kano

Rahoton Vanguard ya ce Gbillah ya zargi Ministocin da karkatar da kudin kafin ayi kasafi da su.

Abin da kundin tsarin mulkin kasa kuwa ya ce shi ne dole ayi kasafi da kudi kafin a kashe, a nan ma kwamitin ya zargi wadannan jami’ai da saba doka.

Taurin kan Malami da Ahmed ya kai ‘yan majalisar tarayyar su na barazanar su bada umarni a cafke su, idan ba za su kawo kan su gaban kwamitinsu ba.

Duk da wasikun da aka aikawa Ministocin domin su yi wa majalisa karin haske, ba a ga keyarsu ba.

Aikin kwamitin Hon. Mark Tersee Gbillah

An ji labari Kwamitin Hon. Mark Tersee Gbillah ya na bincike a Majalisa domin a iya gano gaskiyar lamarin saidawa kasar Sin gangunan fetur miliyan 48.

Ana zargin manyan gwamnati sun karbi miliyoyi a kasar waje, amma dukiyar ba ta shiga asusun kasa ba. Har yanzu wadanda ake zargi ba su ce uffan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng