Sunayen Jerin Sarakuna, Shehunan da Suka Yi Buda Baki da Shugaban kasa a Makkah

Sunayen Jerin Sarakuna, Shehunan da Suka Yi Buda Baki da Shugaban kasa a Makkah

  • Yayin da ya je ibadar Umrah a kasa mai tsarki, Muhammadu Buhari ya kira taron shan ruwa a jiya
  • Shugaban Najeriyan ya samu damar zama da Shugabanni da malaman addinin Musulunci a Makkah
  • Sarakunan gargajiya sun sha ruwa tare da Buhari wanda wa’adinsa a kan mulki yake zuwa karshe

Saudi - Muhammadu Buhari ya shirya taron buda baki ga malaman addinin musulunci da sarakunan gargajiya a birnin Makkah a kasar Saudi Arabiya.

A wajen shan ruwan da aka yi, Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi cewa Muhammadu Buhari ya yi maganar yadda ya yi mulki ba tare da bambanci ba.

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa ta kawo cigaba a duk wani bangare na kasar nan, ya kuma yi amfani da watan azumi wajen yin kiran a zauna lafiya.

Kara karanta wannan

Ziyarar Umrah: Buhari ya dawo Najeriya bayan shaefe kwanaki 8 a kasar Saudiyya

Jawabin Garba Shehu ya ce Mai girma Muhammadu Buhari ya godewa wadanda suka halarci taron.

Sarakuna sun yi magana

Masu martaba Sarakunan Kano da Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero sun yi magana a taron, suka fadi muhimmancin zaman lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta ce malaman addinin da suka je wajen shan ruwan sun hada da Malam Abubakar Abdulwaheed Sulaiman da Sheikh Al-Kanawi Alhassan Ahmed.

Buhari a Saudi
Muhammadu Buhari da Muhammad 'Dan Sarki Salman Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Dr Bashir Aliyu Umar, Muhammad Kamaluddeen Lemu, Nuruddeen Danesi Asunogie, Abdulrasheed Adiatu da Sheikh Haroun Ogbonnia Ajah sun halarta.

Ragowar shehunan su ne Alhaji Ibrahim Kasuwar Magani, Farfesa Shehu Ahmed Sa’id da Bala Lau.

A wajen shan ruwan an ga Sarkin Bauchi, Rilwan Adamu Sulaiman da irinsu Akadiri Saliu Momoh, Abdulfatah Chimaeze Emetumah, da Isa Sanusi Bayero.

An yi wa Najeriya addu'a

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban EFCC, Gwamnoni, Buratai Suka Fadawa Buhari da Aka Hadu a Saudi

Buhari Sallau ya rahoto cewa kafin nan, Buhari ya hadu da Sarkin Auchi, Aliru H.Momoh da Mai martaba Sarkin Lafiya, Mai shari’a, Sidi Mamman Bage.

Fatima Emetumah ta samu halartar taron, inda aka yi wa adduo’in zaman lafiya tare da yin ban kwana da Buhari da fatan gwamnati mai-ci za ta samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng