Dalibai 8 Da ’Yan Bindiga Suka Sace a Kaduna Sun Kubuta, Gwamna Ya Yaba da Kokarinsu
- Wasu dalibai sun yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan ta’addan da suka sace su a farkon watan nan na Afrilu da muke ciki
- An ruwaito cewa, takwas daga cikin daliban ne suka tsere tare da neman taimakon da ya kai su ga isowa hannun jami’an tsaro
- Gwamna El-Rufai na Kaduna ya yaba da irin kokarin da daliban suka yi na tsira daga hannun ‘yan ta’adda masu cutarwa
Jihar Kaduna - Dalibai takwas na makarantar gwamnati ta sakandare da ke Awon a jihar Kaduna da aka sace sun yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindiga.
An sace daliban ne a ranar 3 ga watan Afrilu a yankin Awon na karamar hukumar Kachia ta jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito
A cewar majiyoyi, daliban sun yi nasarar tserewa ne daga kungurmin dajin da aka boye su wanda ke tsakanin jihar Kaduna da Neja a yankin.
Yadda daliban suke tsere
An tattaro cewa, daliban mata sun yi tafiyar tazara kuma ta tsawon kwanaki kafin daga bisani suka gane inda suke, sai suka nemi taimakon a kawo su gida.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da sanarwar da ke tabbatar da kubutar wadannan daliban.
A sanarwar ta ranar Talata 18 Afirilu, 2023, Aruwan ya ce an sanar da gwamnatin jihar labarin kubutar daliban, wanda gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar ya umarci a gaggauta dauko su.
'Yan ta'adda na ci gaba da neman daliban
A cewarsa, yanzu haka ‘yan ta’addan na ta sintiri da binciken kwakwaf a cikin dajin don sake kama daliban da suka tseren, PM News ta ruwaito.
Ya kara da cewa, takwasi daga cikinsu ne sojoji suka dauko, inda a halin yanzu suke karbar kulawar likitoci a asibiti.
Aruwan ya ce, gwamna El-Rufai ya kuma yaba wa daliban bisa jajircewa da nuna kwazon tserewa daga hannun ‘yan ta’addan.
Sojoji sun harbe dan sanda a Borno
A wani labarin, kun ji yadda wasu sojoji suka hallaka wani dan sandan da ke bakin aiki a wani yankin jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Wannan ya faru ne a lokacin da dan sandan ya kama wani soja dauke da tabar wiwi a cikin wata motar da yake ciki.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin kafin daga bisani a dauki matakin da ya dace.
Asali: Legit.ng