Bayan Kai Ruwa Rana a Zabe, INEC Ta Ce Fintiri Ne Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa

Bayan Kai Ruwa Rana a Zabe, INEC Ta Ce Fintiri Ne Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa

  • Rahoton da muke samu daga jihar Adamawa ya bayyana cewa, an ayyana Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar
  • Wannan na nufin, Fintiri zai sake komawa kujerarsa ta gwamna a karo na biyu don sake shafe shekaru hudu yana mulki
  • A baya, an samu tsaiko bayan da aka yi kuskuren sanar da Binani a matsayin wacce ta lashe zaben jihar da aka gudanar

Jihar Adamawa - Wata guda kenan bayan kada kuri’u a zaben gwamnan jihar Adamawa, Gwamna Ahmad Fintiri ya sake lashe kujerar gwamnan jihar, Channels Tv ta ruwaito.

A zaben cike gurbin da aka gudanar ranar Asabar, dan takarar PDP, Fintiri ya samu kuri’u 9,337, yayin da Aisha Binani ta APC ta samu kuri’u 6,513.

Daga karshen zaben gaba daya, Fintiri ya samu kuri’u 430,861, inda ya turmushe ‘yar takarar APC Binani mai kuri’u 398,788 a zabuka biyu da aka gudanar.

Kara karanta wannan

An saka maku ciwon kai: Bayan turmushe Binani, Fintiri ya yiwa 'yan jihar Adamawa jawabi

Fintiri ya koma mulki
Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An sanar da sakamakon zaben Adamawa

A yau Talata 18 Afirilu, 2023 da misalin karfe 5:49 na yamma ne hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben gwamnan, wanda a farko ya zo da rikici na siyasa, Tribune Online ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tun farko, an samu tsaiko a ranar Lahadi kwamishinan zabe na jihar, Hudu Yunusa Ari ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna, wanda hakan ya saba da dokar zabe.

Sashe na 25 na dokar zabe ta 2022 ta bayyana cewa, baturen zabe ne ke da hurumin sanar da sakamakon zaben da kuma ayyana wanda ya yi nasara a jiha.

A wancan lokacin da Hudu ya sanar da zaben, kananan hukumomi 10 kadai aka kawo daga cikin 20, kuma Fintiri ne ke kan gaba da kananan hukumomi bakwai, Binani na da uku.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai: APC ta samu kujeru 134, an fadi kujerun PDP, NNPP, LP da SDP

A bangare guda, shugaban wata kungiyar kamfen ta APC a jihar Adamawa, Sa'idu Njidda ya ce sam an tauye hakkin Binani.

Yace:

"Kawai don macece shi yasa ake wannan, amma gaskiya fa an yi murdiya. Baku ji abin da aka sanar ba, kai ka san da ji akwai wani abu a kasa.
"Amma za mu jira, za mu ji meye za ta dauka na mataki tun da ta tafi kotu tun da fari."

INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben Adamawa

Jim kadan bayan sanarwar, ‘yar takarar APC da masu bin bayanta suka shiga murna, lamarin da ya kawo tsaiko da cece-kuce a jihar.

Daga baya, hukumar zabe ta nesanta kanta da sanarwar Hudu tare da bayyana dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben da aka gudanar.

Yanzu dai komai ya kammala, an sanar Fintiri ya lashe zabe, ba a san meye zai biyo baya daga tsagin Aisha Binani ba.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

A bangare guda, kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ki sauraran karar da ‘yar takara Aisha Binani ta shigar a gabanta game da zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.