Rundunar Yan Sanda Ta Sallami Jami’anta Da Ke Ba Wa Rarara Tsaro
- An kori jami'an yan sandan da ke tsaron shahararren mawakin APC, Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da batun korar jami'an a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu
- Adejobi ya ce an sallami jami'an uku da aka hada da mawakin don ba shi kariya ne daboda barnatar da harsasai
Rundunar yan sandan Najeriya ta sallami jami’anta da ke ba shahararren mawakin siyasa, Daura Adamu Kahutu Rarara tsaro, a ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, Daily Trust ta rahoto.
Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya sanar da hukuncin a hedkwatar rundunar da ke Abuja, ya ce an kori jami’an ne saboda barnatar da harsasai.
A kwanaki ne aka hasko masu tsaron mawakin a wani bidiyo suna harba harsashi a sama yayin da Rarara ke hanyarsa ta shiga motarsa a Kano.
Wannan abu da suka aikata ya haddasa cece-kuke sannan rundunar yan sandan ta sha alwashin daukar mataki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani bangare na sanarwar na cewa:
Bayan korafe-korafe da bincike kan bidiyo da ya yadu a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023, a kafafen soshiyal midiya na izza, rashin sanin makamar aiki, da kuma amfani da makamai ba bisa ka’ida ba da wasu yan sanda daga sashin ba da kariya na musamman (SPU) sashi na 1, Kano suka yi, an kori jami’ai uku daga sashin SPU 1 Kano kan laifin amfani da makamai ba bisa ka’ida ba, cin mutuncin aiki, rashin da’a, da kuma barnatar da harsasai.
“An hada jami’an uku, Sufeto Dahiru Shuaibu, Sajan Abdullahi Badamasi da Sajan Isah Danladi da mawakin don aikin ba shi kariya. Da suke bakin aiki a ranar 7 ga watan Afrilun 2023 a kauyen Kahutu, jihar Katsina, jami’an sun yi harbe-harbe a sama daga makaman aikinsu duk da tsarin aikin yan sanda bai yarda da harbi a iska ba, da kuma yin watsi da hatsarin da hakan zai iya haifarwa ga taron jama’ar da ke wajen harda yara. Wannan ba iya laifi da rashin sanin makamar aiki bane kawai harda tozarta rundunar da kasar baki daya."
Daga karshe rundunar yan sandan ta gargadi jami'anta da su tabbata sun aiwatar da ayyukansu daidai da tsarin doka a duk lokacin da suke bakin aiki.
A wani labari na daban, mun ji cewa jami'an tsaron kasar Ingila sun tsare tare da yi wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi tambayoyi a filin jirgin sama a Landan.
Asali: Legit.ng