Sojoji Sun Kai Sumame Sun Rufe Wasu Gidajen Magajiya a Borno
- Dakarun sojoji sun kai wani sumame a wasu gidajen karuwai da ke a cikin birnin Maiduguri na jihar Borno
- Sojojin sun samu nasarar kulle gidajen karuwan waɗanda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru
- Mutanen yankin sun yaba sosai da sumamen da sojojin suka kai inda suka cw hakan abu ne mai kyau
Jihar Borno - Sojoji sun samu nasarar kai sumame a birnin Maiduguri na jihar Borno kan wasu gidajen karuwai masu ƙananan shekaru.
Aminiya ta rahoto cewa sojojin sun kai sumamen ne a kasuwar Fara da ke a rukunin gidajen Shagari Low-cost a cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Kulle gidajen karuwan na zuwa ne bayan wani rahoton musamman na jaridar Daily Trust ta yi inda fallasa yadda ake yin ayyukan da ba su dace ba a gidajen karuwan.
Jirgin Yaƙin Soji Ya Kai Ɗauki Yayin da Yan Bindiga Suka Kaiwa Mutane Hari da Azumi, Da Yawa Sun Mutu
Mutanen da ke rayuwar a yankin sun tabbatar da cewa sojojin sun kuma cafke wasu mutane a yayin sumamen da suka kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halima Abdul wata mazauniyar yankin ta bayyana cewa:
“Kwanaki biyu da suka wuce, sojoji sun kai sumame a wurin. Ba mu da masaniya kan inda suka tafi da masu laifin”
Ta bayyana cewa al'ummar yankin sun shiga cikin kwanciyar hankali bayan sumamen da sintirin da sojojin suka gudanar a yankin.
“Mun shiga cikin yanayin wahala sosai, an kwashe tsawon shekaru ana muzguna mana amma yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu duba da abinda muke gani." A cewar ta
Solomon Joseph, wani mazaunin yankin ya yaba da sumamen da dakarun suka kai a yankin na su, sannan yayi roƙon da a bar ƴan kasuwan da ke gudanar da sana'o'in su a kasuwar su cigaba da neman na abincin su.
A cewarsa:
"Akwai ƴan kasuwan da suke sana'o'insu a kasuwar Fara, muna rokon sojoji da su bar su su dawo su ci gaba da harkokinsu."
Wani Mutum Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta
A wani labarin na daban kuma, wata ƴar gidan Magajiya ta yi biyu babu bayan wani mutum ya tafka mata aikin damfara.
Mutanen dai ya sulale mata da wayarta sannan bai biya ta haƙƙin ta ba.
Asali: Legit.ng